✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Isra’ila ta kai hare-hare 200 ranar Juma’a

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 184 ta jikkata 589 ranar Juma'a a Gaza inda ta lalata masallatai samda da 260

Isra’ila sun kashe Falasdinawa 184 a hare-hare 200 ranar Juma’a a Zirin Gaza bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hamas.

Hukumomin lafiyar Falasdinu sun ce sojojin sun kuma jikkata mutane 589, akasarinsu mata kananan yara.

Kawo yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 15,000 a Gaza, mafi yawansu kananan yara da mata da kuma tsofaffi.

A safiyar Jauma’a sojojin Isra’ila suka kai hari a wani asibitin yara mai gadaje 200, daya daga cikin tsirarun asibitocin da ke aiki a Gaza.

Sojojin Isra’ial suka dakatar da shigar motocin kayan jin kai shiga Gaza daga iyakar Rafa da ka kasar Masar, har sai abin da hali ya yi, matakin da Hukummin Majalisar Dikin Duniya suka yi Allah wadai da shi.

Sojojin Isra’ila sun kuma ruguza Masallacin Halima da ke Khan Yunis gaba daya a ranar Juma’a — kawo yanzu sun rushe masallatai 88 gaba daya sun lalata barin wasu 174.

A ranar kuma ’yan sandan Isra’ila suka rage yawan Falasdinawa da suka shiga yin Sallar Juma’a a Masallacin Kudus  —wuri na uku mafi daraja a addinin Musulunci —zuwa 3,500 daga 50,000.

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa ta mayar da martani ta harba rokoki a yankunan Isra’ila da suka hada da birnin Tel Aviv, Ashodo da kuma Ashkelon.

A tsawon kwanaki bakwai da bangarorin suka tsagaita wuta, Hamas da Israi’ila sun yi musayar fursunonin Falasdinawa da mutanen da kungiyar ta sace daga Isra’ila.

Isra’ila ta kaddamar da sabbin hare-haren ne a yankin Kudancin Gaza, bayan da farko ta umarci Falasdinawa su koma can domin samun aminci.

A safiyar Juma’a kuma sojojin suka jefa takardun umartar mutanen su bar yankin, inda ba a jima ba kuma suka fara luguden wuta.

A ranar Juma’a ta hallaka ’yan jaridar akalla uku ciki har da wakilin kafar Anadolu ta kasar Turkiyya a yayin da suke tsaka da aiki, da kuma Ismail Thawabteh na kafar labaran gwamnatin Falasdinu.

Montaser Al-Sawaf shi ne jarida Bafalasdine na 73 da Isra’ila ta kashe a tsawon makonni bakwai da Isra’ila ta shafe tana cin karenta babu babaka a Gaza.