✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Isra’ila da Hamas za su tsagaita wuta na tsawon kwana 10

Sai dai za a ci gaba da yaƙin da zarar wa’adin ya cika

Kasar Isra’ila da kungiyar Hamas sun amince su tsagaita wuta na tsawon kwanaki 10, inda kuma a lokacin za a yi musayar fursunonin Falasdinawa 300 da Yahudawan Isra’ila kusan 100.

Jaridar Times of Israel ta kasar Isra’ila ce ta rawaito hakan a ranar Laraba, inda ta ambato wasu majiyoyi daga gwamnatin Isra’ila.

Sai idan wa’adin kwanakin tsagaita wuta ya ƙare, za a ci gaba da yaƙin, kamar yadda jaridar ta rawaito.

Shi ma shafin labaran Isra’ila na Ynet ya rawaito cewa Isra’ila ta ƙuduri aniyar aike wa Hamas sunayen fursunonin da za a yi musayar su.

Kazalika, wani ɓangare na yarjejeniyar ya ce ba za a raba iyaye mata da yara ba a lokacin musayar mutanen.

Jaridar ta Isra’ila ta kuma ce Yahudawan da Hamas za ta saki dole ne su kasance ’yan asalin kasar ta Isra’ila ko kuma mazauna cikin ta.

A tashin farko dai, Isra’ila ta tsara sakin Falasdinawa 150 da zarar aka sakar mata mutum 50.

Dukkan wadanda lamarin ya shafa dai za a sake su ne a cikin kwana hudu, inda akalla za a saki mutum 10 a kullum.

A zango na biyu kuwa, za a saki karin Falasdinawa 150 daga gidajen yarin Isra’ila, inda ita kuma Hamas za ta saki mutum 50 su koma Isra’ila.