✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gawurtaccen Shirin Yaki Da Kwararowar Hamada: Don Allah kar a bari ya kare

Tun a zangon farko na mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olosegun Obasanjo (1999 zuwa 2003} da hadin guiwar kungiyar Tarayyar Afirka da wasu kungiyoyin duniya…

Tun a zangon farko na mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olosegun Obasanjo (1999 zuwa 2003} da hadin guiwar kungiyar Tarayyar Afirka da wasu kungiyoyin duniya masu yaki da kwararowar Hamada, gwamnatin tarayya ta yi aniyar dasa itatuwa a cikin wancan shiri mai taken Garwutaccen Shirin Kandagarkin Kwararowar Hamada, a wasu jihohi 11 da suke jihohin `yan gaba-dai gaba-dai cikin annobar kwararowar Hamada a kasar nan.
Jihohin su ne Gwambe da Bauchi da Borno da Yobe da Jigawa da Kano da Katsina da Sakkwato da Zamfara da Kabbi da Kaduna. Aniyar shirin ne ya karwade kasashen Nahiyar Afirka da suke fama da annobar Hamada.
A karkashin shirin, a wadancan jihohi da aka aiwatar a bara tsakanin watan Agusta zuwa Oktoba, an dasa miliyoyin irin itatuwa masu layi takwas-takwas a jere masu tsawon kilomita dai-dai daga wuri zuwa wuri, a cikin kananan hukumomin da shirin ya shafa, bayan da gwamnatin tarayya ta samar da Naira billlyan 10, don shirin a tsakanin watan Afrilu zuwa na Yunin bara, wadanda daga ciki aka kebe Naira miliyan 310 da aka ba gwamnatocin jihohin, don su tanadi irin itatuwan dasawar.
Kwamitin aiwatar da shirin na kasa, yana karkashin jagorancin Kwamishinan Kare Muhalli na Jihar Zamfara, Alhaji Muktar Lugga.
Don a karfafawa manoma da sauran masu ruwa da tsaki a cikin shirin, bayan jami`an gwamnatocin jihohin da suke cikin shirin, an kuma yi amfani da hakimai  da dagattai da masu ungunni wajen yekuwa da karfafa wa talakawansu guiwa don su karbi shirin cikin sauki. Dadin-dadawa, an tanadi irin itatuwan da za a rika samun kudaden shiga daga gare su, duk shekara, irin su mangwaro da gwaba da kashu da dabino da lemo da dalbejiya, bisa ga la`akari da wuraren da ya kamata a dasa su.
Wani tagomashi da kuma aka alkawarta ma manoman don kara samun nasarar shirin, shi ne tabbacin samar masu da rijiyoyin burtsare da za su rika ban ruwan dashen itatuwan, musamman kasancewar da ma wuraren da aka zaba din, wurare ne da suke fama da karancin ruwan sha, bare kuma wanda za su yi ban ruwan da su, saboda yanayin yankunan nasu suna fama da annobar kwararowar Hamada.
Sai dai kash! Daga rahoton da jaridar Daily Trust, ta ranar 19 ga wannan watan, ta binciko ta buga a shafinta na 48, ta samo cikakkun bayanai a kan matsayin shirin a tsakankanin jihohin Kano da ta dasa gindin itatuwa 425,000; da Zamfara da ta dasa itatuwa 75,000; da Sakkwato da ta dasa itatuwa 200,000, sai ta gano shirin yana kokarin karewa.  
A wancan rahoton kwamishinonin jihohin uku, Alhaji Muhammadu Badawi na Kano da Alhaji Muktar Lugga na Zamfara, shugaban kwamitin shirin da Alhaji Muhammadu Jabbi na Sakkwato, a hirarsu daban-daban, sun tabbatar da cewa matsaloli uku zuwa hudu, suka kawo cikas a cikin shirin baki daya. Na daya sun yi zargin cewa rashin samun kudaden aiwatar da shirin a daidai lokacin da ya dace, ya taimaka matuka wajen mutuwar itatuwan da aka dasa kusan daukewar ruwan daminar bara a tsakanin watan Agusta zuwa na Oktoba. Masana tsirrai da itatuwa sun tabbatar da cewa muddin ana son dashen itace ya kama, to kuwa yana bukatar samun ban ruwa na watanni uku ba kakkautawa.
Na biyu, sun yi zargin cewa lokacin da ruwan saman ya dauke ba a giggina rijiyoyin burtsatsen da za a rika ban ruwan dashen da su ba, wannan ya sanya wasu daga cikin dashen, suka kone kurmus. Dalili na uku shi ne yadda dabbobi, suka cinye ko suka tattake wasu daga cikin dashen da suke kan hanyar wucewarsu saboda rashin shingaye.
Mai karatu, kar ka tona ka ji irin bacin ran da manoman da shirin zai shafa kai tsaye suka nuna, bisa ga irin yadda suka ga tun ba a je ko`ina ba, shirin ya dauko hanyoyin balbalcewa, alhali tun farko an yi ta kwadaita masu irin garabasar da za su samu a cikin shirin, baya ga kara samun kasar noma mai dausayi da kuma ingantuwar karin samun ruwan sama da raguwar gurbatar muhalli.
Masana a kan kwararowar Hamada, sun kiyasta cewa a kididdigar da aka yi a shekarar 1995, an gano cewa Hamada na kara kwararowa cikin kasar nan fiye da 0.7kilomita (kusan kilomita 1), duk shekara. Mai karatu, sai ka kiyasta kwararowar Hamadar daga shekaru 19 da suka gabata, karuwa take ba raguwa ba, don kuwa ba wani abu a kasa da mahukunta suka yi daga wancan lokacin zuwa yanzu, kamar yadda ta bayyana yanzu ga shirin kasa-da-kasa an fara, amma ya kare katsats, tun ba a je ko ina ba.
A ra`ayina, wancan kwamiti da aka dora wa alhakin tafiyar da wannan gagarumin shiri da ke karkashin jagorancin Kwamishinan kare Muhalli na jihar Zamfara, shi ya karya shirin, don ko ba komai, ai ya kamata `yan kwamitin da kwararrunsu na jihohi da suke tafiyar da shirin su san cewa duk itacen da aka dasa yana bukatar ban ruwa na akalla watanni uku, sannan kuma kowane itace daya yana bukatar kariya ta musamman daga barazana, musamman ta dabbobi, amma suka bari aka yi dashen daf da daukewar ruwan damina, ba tare da an tanadi rijiyoyin da za su maye gurbin ruwan sama ba, haka batun kare itatuwan daga barazanar dabbobi.
A zaman `yan kwamitin sun san da haka, kamata ya yi a ce sun shawarci gwamnatin tarayya a kan lallai ta dage shirin zuwa wannan shekarar da muke ciki, wanda hakan zai ba da damar ta tanadi rijiyoyi da shingaye, sannan kuma a yi dashen da zarar damina ta kankama, wajejen tsakiyar watan Yuni, amma suka ki, suka dauki shirin tamfar dashen itatuwan da suka saba yi duk shekara, wanda da zarar an yi ba mai kara waiwayarsa, a zaman kulawa.
To, yanzu itatuwa sun mutu ga kuma shiri yana da muhimmanci. Don haka ya zama wajibi a sake lale, amma dai bai kamata a bari shirin ya mutu murus ba, lallai a waiwaye shi, ko a rage wa Arewa da mutanenta da dabbobinta annobar da ke kokarin raba su da gidajensu da gonakinsu da kiwo. Yanzu kuma ne lokaci, ga masu niyya da kishin talakawansu, domin dai ba annobar kwararowar Hamada a Kudu.