✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata

Ata ya yi barazanar ficewa daga APC muddin aka sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Kano.

Ƙaramin Ministan Gidaje da Tsara Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023 Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara.

Sai dai Ministan ya ce ƙaddarar hukunci daga Allah ne ya sanya a yanzu haka ba shi ke riƙe da madafan iko a Jihar Kanon ba.

Ata ya faɗi hakan ne yayin da yake barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddin ake sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano.

Ministan ya ce kalaman da shugaban jam’iyyar ya riƙa furtawa su ne dalilin da Allah Ya ƙwace mulkin jihar daga hannun jam’iyyar duk da cewa ƙarara ita ce ta lashe zaɓen gwamnan jihar a shekarar 2023.

Aminiya ta ruwaito cewa furucin Ministan na zuwa yayin wani taron ƙusoshin jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Fagge da aka gudanar a Kano.

A cewarsa, “muna sake jaddada aniyar cewa idan suka dawo mana da shi [Abdullahi Abbas], za mu fice daga jam’iyyar.

“Saboda muddin haka ta kasance babu makawa sai jam’iyyar ta sake shan ƙasa. Ba ma tare da irin waɗannan mutane kuma ko mai za faru ba za mu yi tarayya da waɗannan mutanen ba.”

Ata ya bayyana kalaman da Abdullahi Abbas ya riƙa furtawa a matsayin dalilin da jam’iyyar APC a Kano ta sha ƙasa a Zaɓen 2023 — waɗanda ya bayyana a matsayin lafuza marasa kan gado kuma masu munana ladabi ga Allah.

Ya yi gargaɗin cewa muddin aka sake danƙa wa Abdullahi Abbas ragamar jagorancin jam’iyyar to babu makawa sai ta sake shan ƙasa.

“Mun taso an yi mana kyakkyawar tarbiyya, mun san wane ne Allah. Muna girmama malamai da manya saboda haka ba za mu sauka daga kan wannan tarbiyyar ba.

“Amma idan sun dage cewa lallai sai sun dawo da shi [Abdullahi Abbas], za mu fita mu ƙyale musu jam’iyyar kuma na rantse sai jam’iyyar ta sake faɗuwa.”

Minista Ata ya jaddada buƙatar sauya Abdullahi Abbas da wani jagora mai mutunci da daraja muddin jam’iyyar APC tana da burin samun nasara a Jihar Kano.

Kazalika, ya ce Allah ne Yake bayar da mulki ba tasirin yawan ƙuri’u ko dukiya ba.

“Kuri’u ko kuɗi ba sa bayar da mulki hakazalika mutane ba sa yanke hukunci kan wanda zai jagorance su saboda duk wannan lamari a hannun Allah yake.

“Gawuna ne ya yi nasara amma aka murɗe mana zaɓen. Muka garzaya kotu kuma ta tabbatar da cewa an yi mana maguɗi.

“Amma a ƙarshe wanda yake bayar da mulki ya karɓe daga hannunmu saboda ya nuna mana iyakarmu,” in ji Ata.

Wannan dai shi ne karon farko da Ministan ya fito ƙarara ya soki shugabancin jam’iyyar APC a Kano.

Sai dai ana danganta lamarin da yadda wasu ƙusoshin jam’iyyar ke adawa da naɗinsa a matsayin Minista bayan sauke Abdullahi Tijjani Gwarzo da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Bayanai sun ce gabanin zaɓen 2023 an