An binne shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasar Najeriya wanda Allah Ya yiwa rasuwa, Malam Abba Kyari, a makabartar Gudu da ke Abuja.
Tun da farko dai an yi wa marigayin jana’iza bayan isowar gawarsa babban birnin na Najeriya tare da bin ka’idojin da hukumomin lafiya suka gindaya, kamar yadda babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar a kan al’amuran yada labarai Malam Garba Shehu ne ya shaida wa wakilin Daily Trust.
“A kokarin tabbatar da sau da kafa an bi ka’idojin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) da Ma’aikatar Lafiya game da suturta wadanda coronavirus ta yi ajalinsu, za a yi sallar jana’izar a kuma binne shi a sakaye”, inji Malam Garba Shehu.
Coronavirus: Abba Kyari ya rasu
Ganin karshe da aka yi wa Abba Kyari
Ya kuma ce ba za a yi zaman makoki ko karbar gaisuwa ba ta rasuwar.
“Ana kira ga abokan arziki, da dangi, da sauran jama’a su yi wa Abba Kyari addu’ar neman gafara”, inji shi.
Da daren Juma’a ne dai Malam Abba Kyari ya rasu bayan ya kwashe makwanni yana fama da cutar coronavirus, wadda aka yi amanna ya kamu da ita yayin wata ziyara da ya kai Jamus da Masar a watan jiya.
A ranar 24 ga watan na maris ne aka sanar da cewa gwaji ya tabbatar da marigayin ya kamu da cutar, kafin daga bisani ya kai shi wani asibiti a Legas don yin jinya.