✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Gawa’ ta farka ana tsaka da yi mata jana’iza

Ana cikin jana'iza aka lura gawar ta fara numfashi tana kuma motsawa.

Wani mutum da aka sanar ya rasu, ya farka a yayin da ake dab da kai gawarsa makabarta a binne.

Bayan an yi wa gawar wanka an yi mata sutura, sai aka kira ’yan uwa da makusnta su yi bankwana da shi kafin a kai gawar a yi mata janaza.

Ana cikin haka ne wasu daga cikin mahalarta suka lura kamar “gawar” tana numfashi a cikin makarar da aka sanya ta.

A bidiyon abin al’ajabin da ya faru a birnin Hermel da ke Arewacin Kasar Lebanon — wanda aka yada a kafafen sada zumunta — ya ga mutane zagaye da makarar, wata mata tana kuka tana taba ‘gawar’.

Ana cikin haka sai mutane suka lura gawar tana mosti, nan take wasu suka fara danna kirgin mamacin domin farfado da shi.

Daga baya wata motar daukar marasa lafiya ta zo daga asibiti ta duba shi.

Likitoci sun tabbatar cewa yana raye, amma ba su yi bayanin abin da ya sa da farko aka sanar cewa ya rasu ba.

Irin haka ya taba faruwa a bara a kasar Indonesiya inda wata yarinya mai shekara 12 ta farka a asibiti bayan likitoci sun sanar da rasuwarta.

Bayan an kwantar da yarinyar a asibitin ’Dr. Mochamad Saleh Regional Hospital’, daga baya likitoci suka sanar cewa ta rasu.

Bayan kimanin awa daya, sai ta bude ido a lokacin da danginta ke cikin yi wa gawarta sutura domin kai ta makwancinta.

Mahaifinta, Ngasiyo, ya bayyana wa wani gidan talabijin cewa: “Lokacin da ake yi mata wanka sai muka lura cewa dumin jikinta yana karuwa.

“Daga baya sai ta bude idanunta, sai muka ji zuciyarta ta fara bugawa, sai ta fara motsi.”

Sai dai kuma murna ta koma ciki, domin bayan kimanin awa daya kuma ta sake cewa ga garinku nan.

An sake yi mata sutura aka binne ta a makabartar da ke kauyen Lambangkuning na kasar ta Indonesiya.

Likitoci sun tabbatar cewa: “Karamar yarinyar ta farfado bayan da farko an sanar da mutuwarta, a asibitin da aka yi jinyar ta.”