✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaskiyar nada Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniyah

Yadda ake nadin Khalifan Tijjaniyyah da kuma ainihin abin da ya faru a Mauludin Sheikh Nyass

Aminiya ta binciko hakikan abin da ya faru da kuma takaddamar da ta nemi dabaibaye labarin nadin Khalifan Darikar Tijjaniyyah.

Labarin nadin ya fara da samun yabo da kushe daga bangarori, kafin daga bisani shugabannin Darikar su sanar cewa ba haka zancen yake ba, wanda shi ya yamutsa hazo.

Shugabannin Darikar dai sun ce ba su suka sanar cewa an nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II khalifah a lokacin taron ba.

Amma wasu mabiya na ganin sauya maganar aka yi, suna masu zargin cewa sanarwar ta tayar da kura ne tsakanin bangarorin tafiyar.

 

An dade ba a yi irinsa ba

Taron mauludin Sheikh Ibrahim Nyass da aka yi a ranar Asabar a Sakkwato ya tattaro bangarorin darikar suka hadu a wuri daya, abin da aka dade ba a gani ba.

A karshensa ne kura ta tashi kan bayanin da ake cewa daya daga cikin shugabanni ya sanar da Sanusi II a matsayin Khalifa a cikin jawabinsa.

Maganar nada Khalifan Tijjaniya a Najeriya ta fara fitowa ne a zikirin da Juma’a da aka gudanar a gidan Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

 

Babu wanda ya nada Sanusi II

Amma shugabanni sun bayyana cewa kuskuren fassarar aka samu daga bangaren mai tafintar jawabin daya daga cikin jagororin daga harshen Larabci.

Shaikh Makki Inyas wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli a Darikar Tijjaniya, kuma Khalifan Inyas ya musanta nadin Sarki Sanusi II a matsayin Khalifah.

Ya yi bayanin ne a taron manema labarai da ya kira a Sakkwato, inda ya ce zaben abu ne da yake da sharudda wanda ake yi a Najeriya da Senegal.

Ya ce, “Abin mamaki ne a sanar da hakan, ganin shi kansa Sanusi II bai taba neman Khalifancin ba.”

 

Neman kawo rudani

Shi ma a jawabinsa, Ibrahim Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya ce, “Muna godiya ga Allah an taru  kowane bangare na Tijjaniya an yi taron nan daya an yi maraba da Khalifa Inyas wanda shi ne zuwansa na farko a Najeriya.

“Maganar Khalifa da ake yi, harkar nan ta addini ce, kowa ya sani halifa Allah ke yin sa.

“Wasu ne ke son kirkirar matsala a lokacin da ake son kowa ya hada kai da kowane bangare, kamar wannan mauludin abu ne na nuna hadin kai.

“Abin da ya sa hankalin mutane ya tashi, abu ne wanda yadda aka yi shi ba haka aka fassara shi ba.

“Na daya Shaikh Muhammad Makki I kane ne ga Khalifa, ba zai iya nada halifa ba,” kamar yadda ya bayyana.

 

Ainihin abin da Sheikh Makki ya ce

Ya ce abin da Sheikh Makki ya ce shi ne, “Yau ga shi an hadu an yi zikirin Jumu’a, shi dan gidan Inyas ne ga kuma gidan Bayero —waton Abdullahi Bayaro da ya kawo Inyas a Najeriya — jinin Sanusi a tare da mu; Abin da ya fada ke nan.

[Amma bisa kuskurin yin tafinta], “Shi mai fassara sai ya fadi abin da ya fada wanda mu a Tijjaniya ba mu goyon bayan irin wannan; Mu mutane ne masu ladabi da biyayya ba mu son wani ya shiga harkarmu ya kawo wasa a ciki a ji tsoron Allah.

“Maganar halifa in ta taso ana bukatarta don a yanzu a Najeriya ba ta kai ana bukatarta ba,” a cewarsa.

 

Yadda ake nada Khalifa

“Sannan kowa halifa ne inda yake da almajiransa, kowa ya san halifansa da shehinsa da mukaddaminsa, harkarmu ba ta zamani ba ce.

“Sarki Sanusi bai taba zuwa ya ce yana neman Halifanci ba, a yanzu kuma da an ce ga halifa sai wasu sun nuna kin amincewarsu.

“Harka ce in ta taso shugabanninmu malamanmu a Najeriya za su yi shawara su amince da wane ya shugabance mu, sai a rubuta a buga hatimi  a kai Kaulaha, Halifa ya tara ’yan uwanshi sannan a amince,” a cewarsa.

 

An yi amai an lashe

Sai dai wani daga cikin mabiyin darikar ya shaida wa Aminiya cewa yana zargin an sauya maganar ce saboda akwai bangaren ba su aminta da nadin ba.

A cewarsa, bangaren Shaikh Dahiru Bauchi ba su aminta da nadin ba ne saboda suna ganin Shaikh Shariff Saleh ne yafi cancanta da zama Khalifa a wannan lokacin.

“Ni a ganina da su bar masa tun da yana da sha’awa da lamarin ya fi, da da a zo da wani abu da zai iya raba kan tafiyar Tijjaniyah, ba mu fatar hakan,” kamar yadda ya bayyana.