✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai: Yau za a fitar da jadawalin wasan kwata-fainal

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fitar jadawalin wasan Kwata-Fainal na gasar Zakarun Kulob na Turai. Fitar da jadawalin zai gudana ne…

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fitar jadawalin wasan Kwata-Fainal na gasar Zakarun Kulob na Turai.

Fitar da jadawalin zai gudana ne a Hedkwatar Hukumar UEFA da ke Nyom a kasar Suwizilan da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya.  Ana sa ran kafofin watsa labarai na duniya ciki har da na yanar gizo za su nuna yadda jadawalin zai gudana kai-tsaye.

  kungiyoyi takwas ne suka kai wannan mataki da suka hada da Jubentus na Italiya da Liberpool da Manchester City dukkansu daga Ingila da kuma Real Madrid da Sebilla daga Sifen.

Sai AS Roma daga Italiya  da  Bayern Munich daga Jamus sai kuma FC Barcelona daga Sifen.

Kamar yadda jadawalin ya nuna, kowace kungiya za ta iya haduwa da takwararta a wannan mataki.  Ma’ana kungiyoyin da suka fito daga kasa daya za su iya haduwa da juna.  Misali kulob din Real Madrid zai iya haduwa da na FC Barcelona ko Sebilla, kamar yadda kulob din Liberpool zai iya haduwa da Manchester City, kamar yadda AS Roma za ta iya haduwa da Jubentus. 

Za a fara wasannin zagayen farko ne a ranakun Talata 3 da Laraba 4 ga Afrilu mai zuwa yayin da za a yi wasannin zagaye na biyu a ranakun Talata 10 da Laraba 11 ga watan Afrilun inda daga nan ne za a tantance kungiyoyi hudu da za su haye matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal).

Real Madrid ce ke rike da kambun kofin bayan ta lashe sau biyu a jere kuma sau 12 jimilla.