✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai: Ranar Talata za a koma fagen daga

A ci gaba da fafatawa a Gasar Zakarun Kulob na Turai a ranar Talata 3 da Laraba 4 ga Afrilu ne za a ci gaba…

A ci gaba da fafatawa a Gasar Zakarun Kulob na Turai a ranar Talata 3 da Laraba 4 ga Afrilu ne za a ci gaba da fafatawa, inda ake sa ran kungiyoyi takwas da suka rage za su fafata a wasannin kusa da na karshe (Kwata-Fainal) gida da waje.

Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna a ranar Talata kulob din Sebilla daga Sifen zai kece-raini ne da na Bayern Munich da ke Jamus, sai kuma wasa a tsakanin Jubentus na Italiya da kulob din Real Madrid na Sifen. Duk wasannin za su gudana ne a lokaci daya wato karfe 8 saura kwata na dare agogon Najeriya.

A washegari Laraba ce 4 ga Afrilu za a shawo ta a tsakanin kulob din Liberpool da na Manchester City dukansu daga Ingila sai kuma wasa a tsakanin AS Roma na Italiya da kuma na FC Barcelona na Sifen. Su ma wasannin za a yi su ne da misalin karfe 8 saura kwata na dare agogon Najeriya.

A ranakun Talata 10 da kuma Laraba 11 ga watan Afrilun ne za  a yi wasanni zagaye na biyu a tsakanin wadannan kungiyoyi kuma daga nan ne za a tantance kungiyoyi hudu da za su haye matakin kusa da na karshe inda za a fitar da jadawalin kasafta su.

Kulob din Real Madrid ne yake rike da kofin bayan ya lashe sau biyu a jere kuma sau 12 a jimilla.