✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai: Liberpool da PSG sun shiga tsaka-mai-wuya

A ci gaba da fafatawa a Gasar Zakarun Turai zagaye na biyu da aka dawo fage ranar Talatar da ta gabata, kungiyar Liberpool da ke Ingila…

A ci gaba da fafatawa a Gasar Zakarun Turai zagaye na biyu da aka dawo fage ranar Talatar da ta gabata, kungiyar Liberpool da ke Ingila ta hadu da ci daya mai ban haushi a hannun Atletic o Madrid da ke Spain a wasan da ya gudana a kasar Spain.  Sai dai nan da mako biyu Liberpool za ta karbi bakuncin kulob din Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu da hakan zai tantance kungiyar da za ta kai matakin kwata fainal a tsakaninsu.

Haka kuma kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus ya lallasa na Paris Saint Germain (PSG) na Faransa da ci 2-1 a ranar Talatar.

Ana sa ran su ma nan da mako biyu kungiyoyn biyu za su sake karawa a Faransa don a tantance kungiyar da za ta haye zuwa kwata Fainal.

Kuma a shekaranjiya Laraba ce Balencia ta Spain ta sha kashi a hannun Atalanta ta Italiya da ci 4-1, yayin da R.B. Leipzig ta yi wa Tottenham ta Ingila ci daya mai ban haushi a gidanta. Kawo yanzu kungiyoyi takwas ne suka fafata a junansu, yayin da sauran kungiyoyi takwas kuma za su yi nasu wasannin a ranakun Talata da Larabar makon gobe.