✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar zakarun kulob-kulob na Turai: Zan so a cire Arsenal – Mourinho

Kocin kulob din Chelsea na Ingila Jose Mourinho ya ce yana matukar son ganin an cire kulob din Arsenal na Ingila daga gasar zakarun kulob-kulob…

Kocin kulob din Chelsea na Ingila Jose Mourinho ya ce yana matukar son ganin an cire kulob din Arsenal na Ingila daga gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League).  Ya ce dalilinsa shi ne saboda Arsenal din za ta hadu ne da kulob din abokinsa Marco Silba wanda yake horar da Olympiakos na Greece.  Ya ce ya san kocin Olympiakos tun suna kanana don haka yake fatar ganin kocin ya haye da kulob din zuwa mataki na gaba a gasar.
Sai dai shi kansa Mourinho din yana cikin matsala a gasar inda akwai yiwuwar a cire kulob dinsa na Chelsea daga gasar muddin ya samu rashin nasara a wasan da kulob din zai yi da na FC Porto a makon gobe.
Arsenal dai tana matsayi na uku ne a rukunin F.  Bayern Munich ce ta farko da maki 12 sai Olympiakos ta biyu da maki 9 sai Arsenal ta uku da maki 6 yayin da Dinamo Zagreb ke matsayi na hudu da maki 3.  
Idan Arsenal ta samu nasara a wasan, za ta hada maki 9 kenan daidai da na Olympiakos, kuma ya danganta da yawan kwallayen da ta zura a raga kafin ta haye zuwa mataki na gaba. Amma idan Olympiakos ce ta samu nasara a kanta ko kuma suka yi kunnen doki, to an cire Arsenal daga gasar kenan sai badi.