✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Wasanni ta Kasa: Fitilar Hadin-Kai ta isa Gombe

A shirye- shiryen Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Kasa don gudanar da gasar wasanin kasa da ke tafe daga 22 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu…

A shirye- shiryen Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Kasa don gudanar da gasar wasanin kasa da ke tafe daga 22 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu a garin Benin na Jihar Edo wakilan Ministan Wasanni dauke da Fitilar Hadin-Kai (Torch of Unity) sun isa Jihar Gombe.

Da yake bayyana wa Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe makasudin zuwansu Gombe Ko’odinatan Shiyyar Arewa maso Gabas na Ma’aikatar Alhaji Datti Muhammad Kabir, ya ce sun zo Jihar Gombe ce don mika wannan alama ta fitila ga Gwamnan Jihar don tabbatar musu da shigarsu gasar wasannin 32 da za a fafata.

Alhaji Datti Muhammad Kabir, ya ce wannan wasa shi ne karo na 20 kuma Jihar Gombe ta samu shiga bana, wasan da suke sa ran za a ranar  22 ga Maris kuma a bisa shirin da Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta yi zai burge kowa.

Da yake amsar fitilar, Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Dokta Manasseh Daniel Jatau a madadin Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce yanzu wasa ya zama sana’a kuma bayan haka wasannin motsa jiki suna da amfani kwarai ga lafiyar masu yin sa.

Dokta Manasseh Daniel Jatau, ya kara da cewa suna sa ran a samu kwararrun ’yan wasa a nan gaba wadanda za su yi suna asana’ar wasa kamar yadda su J.J. Okocha da Daniel Amokachi suka yi a baya. Don haka ya bukaci matasan su dage su yi kokari su zama masu daukar wasa a matsayin sana’a don su dogara da kansu.

Haka kuma ya yi kira ga matasan da su sa jiki wajen yin wasan domin fitar da Jihar Gombe kunya da kuma samo mata nasara a dukkan wasanin da za su shiga.

Sai Mataimakin Gwamnan ya hori Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Malam Hamza Adamu Soye cewa ya tsaya sosai kada ya bar ’yan wasan su yi sake a bar Gombe a baya.

Shugaban Hukumar Wasannin ta Jihar Gombe, Malam Hamza Adamu Soye, ya ce za su shiga wasanni 16 ne a cikin wasanni 32 kuma suna sa ran samun nasara a dukkan wasanin domin sun shirya.

Malam Hamza Adamu Soye, ya ce saboda kokarinsu na samun zakakuran ’yan wasan tsere sun kai wa Kwamishinan Ilimi ziyara don zakulo masu hazaka daga makarantun sakandaren jihar don su wakilci Jihar Gombe.

Ya kara da cewa bangaren ’yan wasan tseren keke za su kai ’yan wasansu garin Tula don samun horo saboda yanayi irin na wajen za su fi samun horo a wajen yayin da ’yan wasan tsere kuma za su kai su Kaltungo.

Daga nan sai ya ce suna sa ran samun gagarumar nasara a dukkan wasannin da za su shiga saboda karfin gwiwar da suke samu daga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.