✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar wasanni a Benuwai: Tawagar Legas ta sha alwashin zama zakara

Gamayyar kungiyoyin wasannin motsa jiki kimanin 214 da masu horar da ’yan wasa 23 ne za su wakilci Jihar Legas a gasar wasanni makarantu da…

Gamayyar kungiyoyin wasannin motsa jiki kimanin 214 da masu horar da ’yan wasa 23 ne za su wakilci Jihar Legas a gasar wasanni makarantu da za a gudanar cikin wannan wata a garin Makurdi da ke Jihar Benuwe .

Wata takardar sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun hukumar wasanni ta Jihar Legas, Bashir Agunloye ta nuna cewa tawagar ta bar jihar cikin makon da ya gabata don halartar gasar wasannin wadda za a gudanar daga ranar 6 zuwa 16 ga watan Nuwamban shekarar da muke ciki.
Sanarwar ta bayyana cewa tawagar za ta fafata a wasanni 16 wadanda suka hada da wasannin daga nauyi da guje-guje da kokawa da kwallon gwalf da wasan tenis da karet da bal din hannu da bal din Kwando da kuma wasan kwallon sanda.
Ya bayyana cewa daraktan wasanni na jihar ya bayyana cewa tawagar Legas za ta shiga wasannin motsa jiki daban-daban da ta shiga a gasar wasannin da aka gudanar a jihar a watan Mayun shekarar da muke ciki.
Ya yaba wa gwamnana jihar Babatunde Raji Fashola da Kwamishinan matasa da walwalar jama’a Wahid Enitan Oshodi saboda taimako da goyon bayan da suka bayar don ganin nasarar gasar wasannin makarantun da aka gudanar.
‘’Yan wasanninmu suna cikin shiri da koshin lafiya don fuskantar kalubalen da ke gabansu na gasar wasannin da za a gudanar saboda suna ta motsa jiki da yin atisaye tun farkon wannan shekara. Saboda haka muna da tabbacin samun nasara a jihar Benuwe. Kuma na yi imanin cewa za mu wuce matsayi na biyun da muka samu a gasar da ta gabata a shekarar 2013’ In ji shi.
Idan ba a manta ba tawagar Legas ce ta samu nasarar lashe kyautar zinare 49 da azurfa 43 da tagulla 54 inda ta zo na biyu a gasar wasannin da aka gudanar a garin Ilorin da ke jihar Kwara.