Tawagar kasar Brazil ta zama zakara gasar kwallon kafar Olympics ta maza bayan doke kasar Spain da 2-1 a ranar Asabar.
Wannan nasarar ta bai wa Brazil damar samun zinari da kuma kare kambin ta da ta samu shekaru 4 da suka wuce lokacin da ta samu irin wannan nasarar.
- Za a fara yi wa manyan Najeriya rigakafin Coronavirus karo na biyu
- ‘A yi wa Abba Kyari afuwa koda an same shi da laifi’
Ana iya tuna cewa, Brazil ce mai masaukin baki a gasar Olympics ta shekarar 206 wacce aka fafata a birnin Rio.
Kowane bangare na kasashen ya taka rawar gani, inda aka kayatar da ‘yan kallo wajen murza leda mai ban sha’awa.
Matheus Cunha da Malcom ne suka jefa wa Brazil kwallo, yayin da Mikel Oyarzabal ya jefa wa Spain kwallo tilo.
Brazil ce ta fara jefa kwallo a karawar ta hannun Matheus Cunha, yayin da Spain ta farke cin ta hannun Mikel Oyarzabal, abinda ya sa wasan ya zarce zuwa karin lokaci bayan kamala shi da ci 1-1.
A minti 108 Malcolm da ya shiga canji ya jefa wa Brazil kwallo ta biyu, wanda hakan ya bata nasarar lashe wasan.