✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Olamfik: Yau Najeriya za ta kece raini da Japan

A yau ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) da ake kira Dream Team Ib za ta kece…

A yau ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) da ake kira Dream Team Ib za ta kece raini da Japan a kwallon kafa bangaren maza na gasar Olamfik a kasar Brazil.  Sannan a jibi Lahadi ne Najeriya za ta yi wasanta na biyu da Sweden sai kuma a ranar Laraba ta buga wasanta na karshe da kasar Kolombiya kafin a tantance kungiyar da za ta haye mataki na gaba a gasar.
Sauran wasannin da za a yi a yau Juma’a a bangaren kwallon kafa sun hada da Iraki da Denmark, Honduras da Aljeriya sai wasan Brazil da Afirka ta Kudu sai Meziko da Jamus da kuma Fotugal da Ajantina.  Sauran wasannin sun hada Sweden da Kolombiya da  kuma Fiji da Koriya Republic
Kimanin shekaru 20 kenan Najeriya ta samu nasarar lashe lambar zinare a kwallon kafa na maza a gasar Olamfik da aka yi a Atlanta na Amurka.