✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar gwarzon dan kwallon Afirka: An cire sunayen Ahmed Musa da na bincent Enyeama

A ranar Litinn da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ’yan kwallo 10 da za su fafata…

A ranar Litinn da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ’yan kwallo 10 da za su fafata a Gwarzon dan kwallon Afirka ta bana. Sai dai daga cikin sunayen babu sunan dan kwallon Najeriya ko daya. 

Gasar wacce za ta gudana a Abuja a ranar 7 ga watan Janairun 2016 idan Allah Ya kaimu, masu horarwa daban-daban da kuma masu ruwa da tsaki a harkar kwallo wadanda hukumar ta amince da su ne za su kada kuri’a don zakulo gwarzon na bana.
Daga cikin ’yan kwallon da za su fafata akwai Yaya Toure dan kwallon Kwaddebuwa da yanzu haka yake bugawa kulob din Manchester City na Ingila kwallo. Kuma shi ne ke rike da kambun a halin yanzu. Sannan akwai Andre Ayew dan kwallon Ghana da yanzu yake bugawa kulob din Swansea na Ingila. Sauran sun hada da Mohammed Salah dan Egypt da ke wasa a AS Roma na Italiya da Ayman Abdemor na Tunisiya da ke wasa a kulob din FC balence na Sifen da Modather Al Tayeb na Sudan da ke wasa a kulob din Al Hilal na Sudan da Peirre-Emerick Aubemeyang dan Gabon da ke wasa a kulob din Borussia Dortmund na Jamus da kuma Saido Mane dan Senegal da ke buga wa kulob din Southampton na Ingila kwallo. Haka kuma akwai Serge Aurier na Kwaddebuwa da ke kwallo a PSG na Faransa da kuma Sofiane Feghouli dan Aljeriya da ke buga wa kulob din FC balence na Sifen.
Sannan Hukumar CAF ta fitar da sunayen ’yan kwallo 10 da za su fafata a gasar gwarzon dan kwallon Afirka amma wadanda ke buga kwallo a Nahiyar Afirka. Su ma babu sunan dan kwallon Najeriya ko daya a ciki.
Ana sa ran hukumar CAF za ta zaftare sunayen ’yan kwallo biyar nan da ’yan kwanaki masu zuwa don sanar da sunaye biya din da za su fafata a ranar da gasar za ta gudana a Abuja daga kowane bangare watau na wadanda suke kwallo a waje da kuma na wadanda ke wasa a Nahiyar Afirka.