✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Jibi za a yi gumurzu a tsakanin Arsenal da Man United

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni a Ingila da aka fi sani da Firimiya, jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni a Ingila da aka fi sani da Firimiya, jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da takwararta ta Man. United.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasan Arsenal na Emirates.

Wasan zai yi zafi ne ganin kungiyoyin biyu suna fafutikar su kare a kungiyoyi hudu da ke sahun farko a karshen gasar ta bana.

Kulob din Man. United dai yana tashe ganin yadda tun bayan da sabon koci Ole Gunnar Solksjaer ya karbi jagorancinsa kawo yanzu bai samu rashin nasara a gasar ba, hasali ma kunnen doki biyu ya yi kacal hakan ya sa  Man. United ya koma matsayi na hudu.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce take saman teburin gasar da maki 71 bayan an yi wasanni 29, sai Liberpool da ke biye da maki 70 a matsayin ta biyu sai kulob din Tottenham na uku bayan ya hada maki 58 sai Man United Na hudu da maki 56 sai Arsenal a matsayin na biyar bayan ta hada maki 55.

Ke nan Arsenal da ke matsayi na 5 za ta kece raini ne da Man United da ke matsayi na hudu a wasan na jibi, don haka duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta to za a bar ta a baya.