✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Arsenal ta ci Fulham 3-0 a wasan farko

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lallasa Fulham da ci 3-0 a wasan farko na Gasar Firimiyar Ingila. Gabriel Magalhaes da Willian sun dauki hankalin…

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lallasa Fulham da ci 3-0 a wasan farko na Gasar Firimiyar Ingila.

Gabriel Magalhaes da Willian sun dauki hankalin jama’a a karawar ta ranar Asabar – wasansu na farko a kungiyar Arsenal.

Alexandre Lacazette ne ya zura wa Fulham kwallon farko sannan Gabriel Magalhaes ya kara musu kafin daga Pierre-Emerick Aubamayeng ya ci ta uku.

A wasan da Arsenal ta wujijjiga Fulham, tsohon dan wasan Chelsea, William ya taka rawa a dukkannin kwallayen da aka zura wa Fulham, wadda ta sha dakile Arsenal din daga haurawa mataki na gaba.