A jibi Lahadi 1 ga watan Nuwamba ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets za ta kece raini da ta Brazil a wasan kwata-fainal a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da yanzu haka yake gudana a Chile. Za a buga wasan ne da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya.
Eaglets ta kai wannan matsayi ne bayan ta lallasa Austireliya da ci 6-0 a jiya Alhamis. An yi wasan ne da misalin karfe 12 na dare agogon Najeriya watau wayewar garin Alhamis. Ita kuma Brazil ta kai wannan matsayi ne bayan ya doke New Zealand da ci daya mai ban haushi.
Wasan da Najeriya za ta yi da Brazil zai yi zafi sosai, hasalima duniya za ta zuba ido ne ta kalli yadda kasashen biyu za su fafata. A bangaren kwallon matasa Najeriya ce take kan gaba a kan Brazil amma a bangaren manya kuwa Brazil ce kan gaba.
Idan za a tuna a shekarar 1996 Najeriya ce ta lallasa Brazil a gasar Olamfik da ta gudana a Atlanta da ke Amurka inda a shekararce Najeriya ta kafa tarihin lashe lambar zinare a bangaren kwallon kafa a gasar Olamfik.
Kawo yanzu dan kwallon gaban Golden Eaglets bictor Oshiemen ne yake kan gaba wajen yawan zura kwallaye a raga a gasar. Yana da kwallaye bakwai kenan bayan ya zura kwallaye uku daga cikin shidar da Najeriya ta lallasa Austireliya.