✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar BBC-Hausa: Tsokaci da sharhi game da hikayar mata

Kwana ya kare Wani jami’in ’yan sanda ne yana aiki a Legas, kullum idan matarsa ta kira shi a waya, ta ce: “Ina kwana, lafiya,…

Kwana ya kare

Wani jami’in ’yan sanda ne yana aiki a Legas, kullum idan matarsa ta kira shi a waya, ta ce: “Ina kwana, lafiya, yaya aiki?” Sai ya ce mata: “Ga mu muna kwasar ganima.” Rannan sai aka ce masa gobe zai tafi Maiduguri, an yi masa canjin aiki. Matarsa ta kira shi, ta ce: “Ina kwana?” Sai maigidan ya ce: “Kwana ya kare!” Sai matar ta ce masa: “Yaya yarona?” Sai ya ce: “Yaro ya zama maraya.” Ta ce: “Ni kuma fa” Sai ya ce: “Ke kuma kin zama Bazawara, domin an kai ni Maiduguri.”

Daga Ali Legos, 08035827300

 

Zaben uwa

Wani ne suka samu sabani da matarsa sai ta nufi daki, yana zuwa sai ya tarar da ita tana hada kayanta a akwati. Ya ce mata: “Haba wance ke kuwa, ina kuma za ki?” Budar bakinta ke da wuya sai ta ce masa: “Wajen uwata zan tafi.” Shi ma sai ya fara hada nasa kayan, sai ta tambaye shi cewa: “Ina za ka?” Sai ya ce mata: “Wajen uwata zan tafi.” Sai ta ce masa: “Haba, to yanzu ’ya’yanmu guda 7 in ka tafi ina za su?” Sai ya ba ta amsa da cewa: “Su ma su tafi wajen uwarsu.”

Daga Abba Abdullahi Makaman Daura

 

Ribar kafa

Wani Ba’amurke ne ya shiga wani shagon sayar da abinci a Landan, sai ya iske wani mutum bakar fata yana zaune a can wata kurya. Ya isa teburin da ake sayen abincin, ya fito da jikkarsa ta kudi, ya ce wa yaron da ke raba abinci: “Kai mai abinci, ina son in saya wa kowa abinci a shagon nan, amma ban da wancan bakin mutumin da ke zaune a kurya.” Yaron ya amshi kudin, ya ci gaba da rarraba wa kowa abinci amma ya tsallake bakin mutumin, kamar yadda Ba’amurke ya bukata. Shi kuwa bakin mutumin bai ji haushi ba, maimakon haka ma, sai ya kalli Ba’amurken, ya ce masa: “Mun gode!” Wannan abu ya kona wa Ba’amurke rai, sai ya sake jawo jikkarsa, ya ce wa yaron: “Ka kara wa kowa abinci, ka hada masa da kwalbar duk irin lemon da yake bukata, amma ban da wancan bakin mutumin.” Yaro ya yi yadda aka bukace shi, inda bayan ya amshi kudin sai shi bakin mutumin nan ya sake kallon Ba’amurke, ya ce masa: “Mun gode!” Wannan abu ya kara saka wa Ba’amurke haushi, ransa ya dugunzuma, ya ce wa yaro mai raba abinci: “Me ke faruwa da wannan bakin mutumin nan ne? Na saya wa kowa abinci da lemu ban da shi, amma maimakon ya ji haushi, sai murmushi yake, kuma yana yi mani godiya, ko dai mahaukaci ne shi?” Sai yaron ya yi murmushi, ya ce wa Ba’amurken: “Ba mahaukaci ba ne, lafiyarsa kalau; shi ne ma mamallakin shagon abincin nan.”

Daga Rabiu R. Lawal

 

Jahilci

Wata rana wani tsohon Bahadeje ya shigo gari sai ya zauna yana hutawa kusa da mutane, da yara gefe suna wasa. Tsohon nan sai ya yi atishawa, sai wani yaro ya ce: “Yarhamakalla!” Sai wani yaro ya ce: “Yanzu wannan tsohon kake ce wa yarhamakalla?” Shi kuma tsohon nan sai ya ce: “Bar shi, ina jinsa; bari ya kara in hora shi.”

Daga Abbas Sunusi Zariya, 08135835173