Kwamitin shirya gasar rubutun kirkirarrun gajerun labarai na Aminiya ya fitar da sakamakon farko na zakaru 20 da suka yi nasara.
Da yake gabatar da zakarun, Shugaban Kwamitin shirya gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana cewa, “kamar yadda aka sanar, aka kuma yi alkawari a farkon gabatar da wannan gasa, an shirya ta ne domin bukatar samar da ingantattun labarai na nishadi cikin Hausa da ke kunshe da matsalolin da ke jibge a tsarin dimokuradiyya da dambarwar siyasa a Nijeriya.
- ‘Dalilin bullo da Gasar Rubuta Gajerun Labarai ta Aminiya’
- Dalilin da muka kirkiro gasar rubutu ta Aminiya – Farfesa Malumfashi
“Wadannan labarai bayan kammala gasar, idan kuma an buga su a matsayin littafi, ana sa ran su zama wata hanya ta nusar da jama’a, musamman matasa muhimmancin da ke tattare ga inganta tsarin dimokuradiyya da tsaftace siyasar kasa baki daya.”
Da yake bayani dangane da yadda aka faro gasar, da ma yadda zakarun 20 suka samu, ya ce “a halin yanzu an zo gabar kusa da karshe a gasar ta AMINIYA-TRUST da GANDUN KALMOMI da OPEN ARTS suka gudanar a madadin Kamfanin Media Trust Nig. LTD, masu buga jaridar Aminiya.
“A watan Agusta 2020 aka kammala karbar sakonnin wadanda suka nuna sha’awar shiga gasar, wadanda sun kai mutum 268.
“Daga cikin wadannan labarai da aka karba, aka mika wa masana a cikin jami’o’i da sanannun marubuta, maza da mata da suka tato guda 100 da suke ganin su ne suka dace a mika wa wasu kwararru su hudu, wadanda suka fitar da gwanaye guda 20 da za a mika wa alkalai uku da za su fitar da gwarzayen da suka cancanci yabo su 12 da kuma zakarun gasar su uku da za a ba kyaututtuka, kamar yadda aka tsara.”
Farfesan ya ci gaba da bayyana cewa “daga cikin wadanda suka kawo wannan gaba, an samu matasa maza 12 da mata 8, ’yan shekara 20 zuwa 33 da suka nuna hazakar kai gabar ta karshe a wannan gasar.
Matasan da suka kai gabar sun fito ne daga sassa daban-daban, musamman jihohin Katsina da Kano da Jigawa da Gombe da Kaduna da Sakkwato da Neja da Borno da kuma kasar Sin, wato China.”
Ya ce tuni dai aka zabi alkalai uku da za a tura wa wadannan labarai guda 20 domin su tace, su fitar da zakaru da wadanda za a yaba wa.
“Za su yi aikin su kammala a cikin watan Oktoba in sha Allahu. Za a kuma buga littafin da ke dauke da labaran da suka samu yabo da kuma lashe gasar a watan Nuwamban 2020, a kuma bayyana sakamako na karshe a watan Disamba 2020, in Allah Ya kai mu,” inji Shugaban Kwamitin Gasar.
Ya ce a ranar 2 ga watan Janairu, 2021 za a yi wani dan kwarya-kwaryan biki a Kaduna, domin karrama zakarun gasar da mika kyaututtuka da satifiket da kaddamar da littafin da ke dauke da labaran da suka yi zarra.
Zakaru 20 Da Suka Samu Nasara
1-Mubarak Idris Abubakar, Jihar Kano – Tufka Da Warwara.
2-Nasiru Kainuwa Hadeja, Jihar Jigawa – Tsalle Daya.
3-Maryam Umar Sakkwato, Jihar Sakkwato – Kazar Kwanci.
4-Faridat Hussain Mshellia (Mrs. Agwash), Jihar Neja – Zabin Allah.
5-Yaseer Kallah, Jihar Kano – Komai Nisan Dare…
6-Mujaheed Amin Lilo, Jihar Kano – Kawalwalniya.
7-Isma’il Gambo, Jihar Yobe – Ci Ga Rashi.
8-Sadik Tijjani Inuwa, Jihar Katsina – Romon Baka.
9-Salim Yunusa, Jihar Kaduna – Tsaka Mai Wuya.
10-Basira Sabo Nadabo, Jihar Kaduna – Baki Guba Ne.
11-Hajara Ahmad Hussaini, Jihar Jigawa – Igiyar Linkaya.
12-Ubaidah Usman, Jihar Sakkwato – Ranar Kin Dillanci.
13-Rufaida Umar Ibrahim, Jihar Kano – Dimokuraɗiyyar Talaka.
14-A’isha B. Nasir, Jihar Kano – Labarin Asiya Da Sulaiman.
15-Mustapha Sufyanu Jikan Malam, Jihar Katsina – Hassada Ga Mai Rabo.
16-Rufa’i Abubakar Adam, Jihar Gombe – Kotun Allah Ya Isa!
17-Yakubu Sa’idu (bn Saeed), Jihar Jigawa – Fan Taba Sama.
18-Habib Galadanchi (PhD). People’s Republic of China – Baban Najeriya.
19-Saifullahi Lawal Imam, Jihar Kaduna – Rana Daya.
20-Habib Sani Yahya, Jihar Kano – Yanayi.