Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na girke-girke. Akwai hanyoyi da dama wadanda mata ke amfani da su wajen gasa kifi walau tarwada ne ko bargi ko kurungu da makamantansu.
A yau na kawo muku irin namu salon gasa kifi domin samun canji a dandano da kuma yanayin girki.
Za a iya cin wannan girkin da dafa-dukar shinkafa ko da latas ko haka kawai ba tare da an hada da wani abu ba. A ci dadi lafiya.
Abubuwan da za a bukata:
·Kifi karfasa
·Attarugu
·Albasa
·Magi
·Kori
·Kabeji
·Dankalin Turawa
·Koren tattasai
·Tumatir
·Tafarnuwa
·Citta
·Foil paper
Hadi:
A samu kifi karfasa sannan a kankare, a cire dauda da bawo sai a wanke da ruwan dumi ko ruwan kanwa ta yadda karni zai fita sannan a ajiye a gefe ta dan sha iska.
A jajjaga attarugu da citta da tafarnuwa sannan a zuba magi a ciki a kwaba da kori. Sannan a yayyanka tumatir kanana a zuba a sake kwabawa. A fere dankalin Turawa sannan a ajiye a gefe. A dauko wannan kifi karfasa a shafa mata kwabin ciki da baya sannan a sanya a gidan sanyi na minti goma domin hadin ya kame a jikin kifin.
Bayan minti goma sai a ciro, a samu ‘foil paper’ a shimfida kamar tabarma sannan a yayyanka albasa da kabeji sannan a dauki kifin da sauran romon a ciki da kuma dankalin Turawan sai a nade shi tamkar nadin tabarma kamar sau uku. Sannan a sanya a na’ura mai gasa burodi. Sai a rage wutar ta koma tamkar rushi. Bayan minti 30 zuwa 35 sai a sauke, a bari ya dan huce sannan a ci.
Da fatan uwargida ta fahimta kuma za ta gwada don jin dadin iyali.