✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gas zai iya inganta tattalin arzikin Afirka

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Seplat Petroleum Debelopment, Dokta Chukwueloka Orjiako ya ce iskar gas tana da damar canja fasaliin tattalin arzikin Afirka idan aka…

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Seplat Petroleum Debelopment, Dokta Chukwueloka Orjiako ya ce iskar gas tana da damar canja fasaliin tattalin arzikin Afirka idan aka yi yi amfani da ita  yadda ya kamata.
Orjiako ya bayyana haka ne a wurin taron kasuwanci na Afirka da Singapore da Kamfanin International Enterprise (IE) ya shirya a Singapore, inda shi da sauran masu jagorantar tattaunawar suka nuna matsalolin da suke Najeriya da Nahiyar Afirka .
Orjiako ya nanata cewa matsalolin da kasar nan ke ciki na faduwar farashin man fetur da tashin farashin Dala da hauhawar farashin kayan masarufi abubuwa ne da suke nuni da cewa ya kamata a canja hanyoyin fadada tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce “Labari mai dadi shi ne, Najeriya tana bin hanyoyin da suka dace ta hanyar cire tallafin man fetur da kyale Naira ta kwaci kanta. Abin da ya kamata yanzu shi ne a tabbatar an saka kudaden da aka tara a wurin da ya kamata kamar habaka masana’antu da noma da ci gaban kasa.  Iskar Gas ita ce kan gaba wajen samar da wannan canjin domin a yankin Afirka, matsalar wutar lantarki ita ce babban abin da ke hana ci gaba. Matsalar wuta babbar matsala ce wadda idan aka gyara ta za ta dawo da masu saka hannun jari.”
Ya ce babbar manufar kasuwancin Kamfanin SEPLAT shi ne karfafa harkar kasuwancin iskar gas don cimma manufar kamfanin na bunkasa harkar gas, ya ce a shekara biyu da suka wuce kamfanin ya ninka iskar gas din da yake samarwa zuwa tan  300, kuma idan aka kaddamar da kamfanin gas na OBEN da zai rika samar da tan 150 a kowace rana, zai kara gas din da kamfanin ke samarwa zuwa tan 500 a kullum nan da karshen bana.
A yanzu haka, Kamfanin SEPLAT na samar da kashi 30 cikin 100 na iskar gas din da ake amfani da shi a gidaje  kuma akwai tsare-tsaren samar da iskar gas ga Najeriya da kuma Afirka ta Yamma.
Shugaban na SEPLAT, ya tabbatar da cewa SEPLAT a shirye yake domin fuskantar canje-canjen da babu makawa sai sun faru a Najeriya da kuma yankin Afirka duk da matsalolin da ake ciki a yanzu.
A game da matsalar samun lasisin man fetur a kasar Afirka ta Kudu inda Bonang Mohale ya nuna cewa akwai dimbin albarkatun man fetur da iskar gas da manyan kamfanonin mai na duniya kamar su Shell ke binicke da ke jibge a kasa, zai bukaci zuba jari.
Kuma an kara nuna cewa gwamnatoci ba su da isassun kudi da fasahar da ake bukata domin hako su don haka abin da ya fi dacewa a ba wa kamfanoni wadanda suke da jari da kwararru damar daukar wannan nauyi ta yadda kasashen za su samucin gajiyar albarakatun ta hanyar samun kudin shiga daga haraji da samar da aikin yi ga jama’arsu da kuma bunkasar tattalin arzikinsu.
Orjiako wanda kamfaninsa ya fara mallakar rijiyar mai daga IOC a yankin Neja-Delta a shekarar 2010, kuma daga baya ya samu wani lasisin biyu daga kasuwar zuba jari ta Najeriya da ta Landan a shekarar 2014, hakan ya sa kamfanin  SEPLAT ya zama kamfani na duniya kuma wani babban jigo a yankin Afirka a fannin harkar fetur da iskar gas, ya nanata cewa  Kamfanin SEPLAT ya sake karfafa gininsa kan wanna dama da ya samu wajen samar da ci gaba sosai a wasu bangarori na kamfanin inda ya kafa tarihi mai kyau a wajen aiki da zaman lafiya da jama’ar yankin da yake zaune, da kuma samar da yanayin aiki da ya fi dacewa.