✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gary Nebille ya zama sabon kocin balencia

A shekaranjiya Laraba ne kulob din balencia na Sifen ya bayar da sanarwar nada tsohon dan kwallon Manchester United da ke Ingila Gary Nebille a…

A shekaranjiya Laraba ne kulob din balencia na Sifen ya bayar da sanarwar nada tsohon dan kwallon Manchester United da ke Ingila Gary Nebille a matsayin sabon koci.
Kulob din ya ce ya nada Nebille ne a matsayin koci har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Nebille ya maye gurbin tsohon kocin kulob din ne mai suna Nuno wanda ya yi ritaya a ranar 29 ga watan jiya.
Shi dai Gary Nebille ya buga wa Manchester United wasa ne a tsakanin shekarar 1992 zuwa 2011 watau ya shafe kimanin shekara 19 kafin ya bar kulob din.
Kulob din balencia yana buga wasa ne a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani La-Liga kuma zai hadu da kulob din FC Barcelona ne a gobe Asabar a cigaba da gasar.