✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwan Kaita ya bayar da kyautar maganin sankarau

A ranar Asabar ce Garkuwan Kaita Alhaji Isma’ila ’Yandaki ya bayar da gudunmawar maganin sankarau da wasu magunguna ga asibitocin da ke karamar Hukumar Kaita. …

A ranar Asabar ce Garkuwan Kaita Alhaji Isma’ila ’Yandaki ya bayar da gudunmawar maganin sankarau da wasu magunguna ga asibitocin da ke karamar Hukumar Kaita. 

Alhaji Isma’ila ya ce, ya bayar da magungunan ne domin bayar da nasa tallafin ga karamar hukumar a matsayinsa na dan karamar hukumar. 

Ya ce, wajibin kowane dan kasa ne da ya kawo tallafinsa domin ciyar da kasa da al’umma gaba maimakon dora wa gwamnati komai alhali Allah Ya hore wa mutane abin da za su bayar da taimakonsu ga al’umma. 

“Yanzu lokaci ne na zafi da ake fuskantar barazanar ciwon sankarau musamman a karkara, wannan ya sa na ga ya dace in bayar da tawa gudunmawar ta wannan fuska ba don gwamnati ta gaza ba, a’a aiki ne da ya rataya a kan kowa ya bayar da tallafi ba sai magani ba koda shawara tagari,” inji shi. 

Garkuwan Kaitan ya ce, lura da kuduri da manufofin gwamnatin Masari ta fuskar inganta kiwon lafiyar jama’a inda gwamnatin ke ware kudi domin gyara asibitoci, yana da kyau duk wani mai kishin Jihar Katsina ya shigo domin bayar da tasa gudunmawar.

Shugabar riko ta karamar hukumar, Hajiya Umma Abdullahi Mahuta ta yaba wannan tallafi na dubban nairori ga al’ummar karamar hukumar a abin da ya shafi kiwon lafiya. 

Ta tabbatar da cewa, sakon wannan matashi mai kishin jama’arsa zai isa ga jama’a da kuma yin amfani da shi ta yadda ya dace. Sai ta yi kira ga sauran masu hali su rika shigowa suna tallafa wa al’umma.

Sarkin Sullubawan Katsina Hakimin Kaita Alhaji Abdulkarim Kabir cewa ya yi, Alhaji Isma’ila ya cika Garkuwan Kaitan. 

“Samun matashi irinka wanda ba mai rike da wani ofis ba ne a gwamnatance a ce yana irin wannan aikin a wannan lokacin gaskiya sai dai-daiku. Saboda haka, ba masarautata ba, al’ummar karamar Hukumar Kaita baki daya na alfahari da kai, kuma muna yi maka godiya da addu’ar fatan alheri,” inji shi.

Wadannan magunguna an rarraba su ne ga asibitocin Dankama da Kaita da ’Yandaki.