Dalibai tara na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da masu garkuwa da mutane suka kama a hanyar Kaduna zuwa Abuja kwana shida da suka gabata sun kubuta bayan ’yan uwansu sun biya kudin fansa.
Aminiya ta samu cewa sai da ’yan uwan kowanne daga cikin daliban masu nazari a Sashen Harshen Faransanci na Jami’ar suka biya sama da N500,000 domin neman ’yancinsu a wani daji daura da kauyen Maru na Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
- Za mu ba ’yan kabilar Igbo kariya a Kano —Sarkin Bichi
- ’Yan bingida sun yi garkuwa da Rabaran a Abuja
- Kotu ta tsare Sanata Ali Ndume a kurkuku
Daliban tara na daga cikin wasu mutum 12 da suka yi shatar wata motar bas mai daukar mutum 18 zuwa ‘Kauyen Faransa’ da ke Legas domin halartar wani shiri na kwarewa a kan yaren Faransanci.
Masu garkuwar sun yi musu kofar rago ne a tsakanin garuruwan Akilubu da Gidan Busa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadin da ta shude inda suka datse musu hanya suka bude musu wuta.
Biyu daga cikin daliban sun tsere da raunin harsashi, yayin da maharan suka kyale wata daliba da suka ce ta ci albarkacin jaririnta na goye.
Direban motar, Nurudeen Muhammad wanda shi ma ya tsallake rijiya da baya, ya tabbatar da cewa dalibai tara maharan suka sace sabanin takwas da a baya aka ruwaito.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun nemi miliyan N270 a matsayin kudin fansa — miliyan N30 a kan kowane dalibi.
Bayan shafe kwanaki ana sasanci da ’yan uwan daliban, masu garkuwar sun tuke a kan adadin kudin fansa daban-daban da za a biya.
Christian John, wanda ’yar uwarsa, Elizabeth daya ce daga cikin daliban, ya tabbatar ’yar uwarsa ta kubuta ta koma gida lafiya bayan an biya kudin fansarta.
Duk da cewa ya ki bayyana nawa suka biya, ya tabbatar cewa tana fama da gajiya kuma cike take da koshin lafiya da farin cikin saduwa da ’yan uwanta.
Kakakin Jami’ar Ahmadu Bello, Auwalu Umar, shi ma ya tabbatar da sako daliban a daren ranar Asabar amma daga bai yi karin bayani ba.
Wasu daga cikin ’yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su sun shaida wa wakilanmu cewa gwamnati ko hukumar jami’ar ba su yi ruwa da tsaki ba wajen sasanci da neman ’yancin daliban.
Yunkurin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ci tura saboda bai amsa kira wayarsa ba.
Yadda muka biya kudin fansa —’Yan uwa
Iyalan daliban sun shaida wa Aminiya cewa an umarce su da su hallara a wani daji a Karamar Hukumar Chikun sannan aka rika ba su umarni hanyoyin da za su bi.
Daya daga cikinsu, wanda ya kai N500,000 na fansar ’yar uwarsa ya ce “tamkar lokaci guda aka ba mu mu kawo kudin fansar.
“Kimanin mutum 12 aka saka a daren ranar Asabar wanda daga cikinsu ne akwai daliban 9; takwas mata da namiji daya”.
“Kowane dangi sun tafi da kunshin kudin fansa a cikin jaka daban-daban kuma aka rika ba mu umarnin yadda za mu yi”, inji shi.
Wani da ya kawo N800,000 a matsayin kudin fansar ’yar uwarsa ya ce, an kayyade adadin kudin fansa daban-daban da ’yan uwan daliban za su kawo kuma mafi karanci shi ne dubu dari biyar.
“Wasu sun biya N700,000, wasu N800,000, wani ma Naira miliyan daya aka biya, amma mu dai N800,000 muka biya domin kubutar da ’yar uwarmu”.
Da yake bayyana yadda ta kasance tiryan-tiryan, ya ce “idan kuna tafiya daga Kaduna zuwa Abuja bayan an wuce sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC, akwai wata fitila mai amfani da hasken rana a daidai wani kauye da ake kira Dutse.
“Daga gefe guda kuma akwai wata hanya mai kwalta da ta shiga har Gwagwada amma kafin mu isa Gwagwada, akwai wata hanyar da za ta mike har kauyen Maro.
“A kan hanyar zuwa Maro ne muka saki hanya muka nutsa cikin daji.
“Muna cikin mummunan tashin hankali a kasar nan domin kuwa wannan abu ya faru ne a kusa da sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC.
Mun shiga Mummunan tashin hankali da firgici
“Mun hadu da jami’an tsaro wadanda ke sintiri a yankin yayin da muke kan hanya sai suka tambaye mu inda za mu saboda ganin yadda dare ya yi.
“Mun sanar da su cewa muna kan hanyarmu ta kai kudin fansa domin neman kubutar da ’yan uwanmu, amma sai jami’an tsaron suka yi mana fatan alheri da samun nasara”, inji shi.
“Mun yi tafiya ta kusan minti talatin a cikin dajin sannan sai muka riski wasu mutane a kan babura kuma suka ce mu hau.
“Bayan mun hau mun yi wata tafiyar ta kimanin minti talati muna nutsawa cikin daji”.
Ya ce bayan sun yi tafiya mai nisan gaske a cikin dajin, sai wasu mutane rike da makamai suka zagaye su kuma suka umarci da su daga hannayensu sama.
“Mun yi kamar yadda suka umarce mu saboda suna rike da makamai sosai, don haka suka binciki jikinmu inda bayan sun kammala, sai suka tattara kudin suka kirga domin tabbatar da cewa sun cika kuma daga nan suka saki wadanda lamarin ya rusta da su.
“Sun umarci da mu hau layi kuma suka rika kira da karbar kudin daya bayan daya.
“Idan aka tabbatar kudinka sun cika, sai ka ambaci sunan wanda ka zo fansa, sannan sai a kira sunansa daga nan sai ka koma gefe a yi wa na bayanka”, inji shi.
“Ana tsakar haka ne wasu daga cikinmu suka samu damar tattaunawa da masu garkuwar, inda wani daga cikinsu ya ce shi tsohon ma’aikacin tsaro ne wanda bayan ya bar aiki ya shiga kungiyar yayin da wasunsu suka yi ikirarin cewa daga kasar Nijar da Kamaru suke”.
Majiyar ta shaida wa Aminiya cewa daliban da sauran mutum uku da aka sako da misalin karfe 10.00 na daren ranar Asabar, ba su isa kwanar Abuja ba har sai karfe 2.00 na dare.
An lakada mana duka mun kwana a ciyawa —Dalibai
Wasu daga cikin daliban sun shaida wa Aminiya cewa wadanda suka yi garkuwa da su sun lakada musu duka saboda gazawar iyayensu wajen biyan kudin fansar da aka nema.
Wani dalibi ya ce an biya kudin fansar takwas daga cikinsu, inda kuma aka saki cikon na taran saboda tausayawa.
“Wadanda suka yi garkuwa da mu sun gaza samun damar tattaunawa da ’yan uwanta, lamarin da ya sa suka yi mata barazana da kisa amma kuma a karshe yayin da muke daf da tafiya, sai suka ce ta biyo mu”, inji dalibin.
“Sun jibge mu kuma sun yi mana baraza, amma ba kamar yadda suka yi wa mazan da ke cikinmu ba.
“Mun rika kwana a sarari, a kan ciyawa kuma suka rika umartar mu da mu dafa abinci.
“A wasu lokutan mun ci shinkafa da doya, kuma wasu lokutan mun ci kwadon gari da kuli-kuli.
“Babu tsaftataccen ruwan sha amma babu yadda muka iya haka muka rika sha saboda mu rayu”, inji ta.
Wata dalibar kuma cewa ta yi ta kamu da zazzabin cizon sauro, inda ta shaida wa wakilanmu cewa dajin akwai sanyi kuma cike yake da sauro inda akasarinsu suka rika rawar dari idan dare ya yi.
“Sun cakuda mu wuri guda kuma sun saki wasu a ranar Juma’a amma mu 12 da muka rage sai a ranar Asabar suka sake mu.
“Ba zan taba mantawa da wannan lamari ba, kuma ina addu’a kada wani ya sake fuskantar irinsa saboda tsananin munin da ke tattare da shi”, inji ta.
Sai dai ta ce saboda ganin yadda suka kasance dukun-dukun, masu garkuwar sun ba su kyautar naira dubu talatin domin sayen sabulun da za su tsaftace kansu da kayan jikinsu.