✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar Mutane: Sheikh Gumi ya ziyarci garuruwan da suka yi kaurin suna a Kaduna

Sun tabbatar da cewa babban kalubalen da suke fuskanta a rayuwa shi ne rashin ilimi.

Shahararren malamin nan na addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ziyarci wasu garuruwa da suka yi kaurin suna wajen sace-sacen mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Aminiya ta samu cewa wuraren da babban malamin ya ziyarta sun yi kaurin suna kasancewarsu tamkar wata cibiya da matafiya ke fada wa komar masu garkuwa da mutane.

Da yake gabatar da jawabai cikin garin Jere a gaban dimbin jama’ar da suka kasance Fulani, Sheikh Dokta Ahmad Gumi ya bayyana damuwa kan yadda duhu na jahilci ya yi musu mummunan lullubi.

A cewarsa, hanya daya da za ta magance matsalar da ke addabar su shi ne samun ilimin zamani da na addinin Islama.

Ya buga babban misali kan yadda ayar Al-Kur’ani ta farko da aka saukar wa Annabi Muhammad (S.A.W) ta nuna muhimmancin neman ilimi.

Sashen Fulanin da suka halarci taron

Sheikh Gumi ya ce duk da ba wani karfi gidauniyarsa ta da’awar Sunnah ta ke shi ba, amma zai gina makarantu gwargwadon hali da za a rika karantar da addinin Islama.

Ya kuma ce za a zabi wasu daga cikin Fulanin wadanda za a rika gabatar musu da laccoci da horaswa domin su koma su rika karantar da al’ummominsu.

Ya ce za a kafa wani kwamiti wanda Fulanin za su rika shigar da korafin duk wani rashin adalci da gwamnati ta yi musu domin a nema musu hakkinsu.

Wasu daga cikin shugabannin na Fulani da suka zanta da Aminiya sun tabbatar da cewa babban kalubalen da suke fuskanta a rayuwarsu shi ne rashin ilimi.

Sashen Fulanin yayin sauraron Sheikh Gumi yana gabatar da jawabai

A cewarsu, an yi watsi da su ba tare da an kula da iliminsu ba ko tsaronsu ballantana a sama musu ababen more rayuwa.

Daga cikin tawagar da ta ziyarci makiyayan akwai babban limamin masallacin Sultan Bello, Dokta Sulaiman Mahmud, da wakilai na kungiyoyin malamai da dalibai, da kuma jami’an tsaro.

Sheikh Gumi ya kuma raba wasu littafan Musulunci da za su taimaka wa Fulanin sanin addininsu.