Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana cewa ba zai sayar da shahararren dan kwallonsa Gareth Bale ba ga kulob din Manchester United da ke Ingila ko a wane irin farashi ne.
Kulob din ya ce rade-radin da ake yadawa cewa ciniki ya kusa kayawa na sayar da Bale ga kulob din United ba gaskiya ba ne.
Shi dai Gareth Bale, kulob din Madrid ya sayo shi ne daga kulob din Tottenham na Ingila kimanin watanni 16 da suka wuce a kan Fam miliyan 85 a cinikin da ba a taba yin irinsa a tarihin kwallon kafa ba kawo yanzu.
Shugaban kulob din Madrid Florentina Perez ya ce “ba mu taba samun wani tuntuba na sayar da Bale daga kulob din United ko wani kulob na daban ba kawo yanzu, hasalima ko nawa aka taya dan kwallon ba za mu sayar da shi ba don muna bukatarsa a halin yanzu”.
Shi kuwa Bale a lokacin da aka yi hira da shi a ranar Talatar da ta wuce jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin Madrid da na AC Milan da ke Italiya a wasan sada zumunta a Dubai inda Madrid ta sha kashi da ci 4-2, ya ce ba ya tunanin zai canza sheka zuwa kulob din Manchester United don yana jin dadin zama a Madrid. Hasalima sai a shekarar 2019 kwantaraginsa za ta kare.
Tun a shekarar 2013 Kulob din United ya so ya dauke Bale daga Tottenham amma kulob din Madrid ya yi masa shigar sauri.
Bale dai ya taimakawa Madrid lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) da kofin Sarki da kofin Super Cup da kuma kofin Club World Club a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014. Ya zura kwallaye 11 a raga a gasar La-Liga ta bana al’amarin da ya sa kulob din yake samun tebur a halin yanzu.
Gareth Bale ba na sayarwa ba ne -Real Madrid
Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana cewa ba zai sayar da shahararren dan kwallonsa Gareth Bale ba ga kulob din Manchester United…