✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Garba Shehu ya warke daga cutar Coronavirus

Ina rokon Allah ya kawo waraka ga dukkan masu fama da cutar.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya warke daga cutar Coronavirus.

Hadimin shugaban kasar da kansa ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Da yake yi wa Allah godiya, Malam Garba ya kuma roki Mai Duka ya tunkudo waraka ga dukkan wadanda suke ci gaba da fama da cutar.

A baya bayan nan dai hadimin shugaban kasar ya sanar da cewa alamomin sun cutar sun bayyana a tattare da shi, lamarin da ya sanya ya kebance kansa daga shiga cikin mutane duk da cewa ba ta yi masa mugun kamu ba.

Wasu bayanai da suka bulla a ranar Asabar sun bayyana yadda cutar ta yi dirar mikiya a Fadar Gwamnatin Najeriya, inda cikin wadanda suka kamu da ita har da dogarin shugaba Buhari, wato Yusuf Dodo da babban jami’in tsaron fadar, Aliyu Musa.

An kuma ruwaito cewa Ministan Yada Labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed na cikin wadanda suka kamu da wannan shu’umar cuta, sai dai tuni ministan ya musanta hakan.

Aminiya ta ruwaito cewa, cutar ba ta yi wa wadannan jami’ai mugun kamu ba, la’akari cewa duk sun karbi cikakkiyar allurar rigakafinta.