✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gani ya kori ji: Kisan matafiya; Auren Yusuf Buhari; Rikicin Afghanistan

Kayatattun hotunan abubuwan da suka faru a wannan makon.

A makon nan mai karewa ne aka kashe matafiya a garin Jos, aka daura auren dan Shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf, Shugaban Kasa kuma ya sanya hannu a Dokar Man Fetur da sauransu.

Ga wasu hotunan kayatattun abubuwan da suka faru a makon ciki har da rikicin kasar Afghanistan da ganawar Buhari da Manyan Hafsoshin Tsaro. Gani ya kori ji.

‘Yan kasar Afghanistan sama da 600 sun yi wa jirgin dakon kayan sojin Amurka cikar kwari domin tserewa zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa bayan Taliban ta kwace mulki a kasarsu. (Hoto: Defense One).
Gwarwakin wasu daga cikin matafiyan da aka kashe a Harin Jos
Gwarwakin wasu matafiya da aka kashe a unguwar Gada-Biyu a garin Jos a hanyarsu ta dawowa daga taron addini a garin Bauchi. (Hoto: Ado Abubakar Musa).
Wasu matasa da aka yi wa alkawarin ladan Naira 200 su ketare rafi da wani babur bayan da gadar da ta hada al’ummomin Dafa da Tunga-Gwomani a Karamar Hukumar Kwali ta Yankin Babban Birnin Tarayya ta karye. Gadar ta rufta ne bayan an tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin ranar Talata. (Hoto: Abubakar Sadiq Isah).
Jarumin Kannywood Garzali Miko ya angwance da da amaryarsa Habiba, a ranar Juma’a a Kaduna.
A cikin makon ne Kudurin Dokar Man Fetur (PIB) ya Zama Dokar Man Fetur (PIA 2021) bayan shekara 10 ana kai-koma a kai. (Hoto: Gwamnatin Najeriya).
Ministan Sadarwar, Isa Ali Pantami ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi ta’aziyyar kisan gilla da aka yi wa mabiyan shehin malamin kusan 30 a Jos, Jihar Filato. (Hoto: Gwamnatin Najeriya).
Manyan Shugabannin Tsaro sun yi zaman farko da Shugaba Buhari bayan dawowarsa da daga Landan, a yayin da ‘yan Boko Haram sama da 1,000 tare da iyalansu suka mika wuya ga sojojin Najeriya. (Hoto: Gwamnatin Najeriya).
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya tsere daga kasar bayan kungiyar Taliban mamaye fadar gwamnatin kasar da ke birnin Kabul, shekara 20 bayan Amurka ta jagoranci hambarar da gwamnatin kungiyar a kasar. (Hoto: AP).
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Tsohon Shugabannin Najeriya da Nijar Goodluck Jonathan da Mahamadou Issoufou da sauran manyan mutane sun halarci daurin auren dan Shugaban Buhari, Yusuf, wanda ya auri ‘yan Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Nasir Ado Bayero. (Hoto: Gwamnatin Najeriya).
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ziyarci Shugaba Buhari a Fadar Shugabn Kasa da ke Abuja.
Kungiyar Taliban ta bukaci mata su shigo cikin gwamnatinta a kokarinta na nuna sassaucin ra’ayi bayan ta karbi mulki a Afghnistan. (Hoto: AP).
Bayan rasuwar dattijon kwarai, Ahmed Joda, Buhari ya ziyarci Lamidon Adamawa a ranar Juma’a domin yi masa gaisuwar ta’aziyya. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).