✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

GANI YA KORI JI: Kayatattun hotunan wasu abubuwa da suka faru

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar…

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku: 

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, yayin da yake karbar takardar yarjejeniya tara da aka kulla tsakanin Najeriya da kasar Spain a ranar Litinin 1 ga watan June 2023 a kasar Spain.

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abuabakar, yayin da ya kai ziyara gidan tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, domin samun goyon bayansa bayan kammala zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP, wanda Atikun ya lashe.

 

Wani dan bumburutu ke nan yayin da yake dan hutawa a gefen hanya bayan ya gaji da neman mai sayen mai ya rasa a kan babbar hanyar Jabi a Abuja. Hoto: Onyekachukwu Obi

 

Mai neman takarar shugabancin kasa, Bola Ahmed Tinubu, yayin da yake fuskantar tambayoyi daga kwamitin tantance ’yan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.

 

Yadda ake sasantawa bayan an samu karo tsakanin mai babur mai kafa uku da wani mai mota a kan kwanar babban ofishin Aminiya da ke Abuja.

 

Yadda wuta ta kama a wani gidan man kamfanin AA Rano da ke titin Murtala Muhammad, daura da otel din Central da ke Kano.

 

Wani daliget din jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna ya raba kudi Naira miliyan bakwai da ya samu daga hannun masu neman takara a zaben 2023 ga marasa galihu.