Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya roki gafarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa abin da ya kira da ‘kuskuren da aka yi baya’ na kokarin hana Buhari yakin neman zaben Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar APC a shekarar 2014 a fikin wasa na Sa Abubakar Tafawa Balewaa lokacin yana Gwamnan Jihar.
Malam Isa Yuguda wanda ya yi Jawabi a madadin manyan ’yan siyasar jihar 18 da suka koma APC, a wurin gangamin yakin zaben Shugaban Kasa na shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a Bauchi a ranar Asabar da ta gabata, ya bai wa Shugaba Buhari tabbacin cewa, “Yanzu na dawo cikin APC, za mu yi aiki tare domin tabbatar da nasarar APC a zaben 2019 da ke tafe,”
Yuguda ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Bauchi bisa ayyukan raya kasa da suke gudanarwa.
Tun farko a jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa game da nauyin da aka dora masa na jagorancin kasar nan, ya rike amana cikin gaskiya, sannan ya yi alkawarin ci gaba daga inda ya tsaya idan aka zabe shi a karo na biyu.
Bayan daga hannun Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da sauran masu takara Majalisar Dokoki ta Kasa, Shugaba Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su zabi APC daga sama har kasa, don tabbatar da samar musu da saukin rayuwa da ci gaba da yin aiki tukuru da zai kai kasar na ga tudun mun-tsira.
Shugaba Buhari ya ce dukan alkawuran da ya yi wa ’yan Najeriya a 2014 ya samu gagarumar nasarori a kansu, sannan ya ce zai kara zage damtse wajen yaki da cin hanci da rashawa da shawo kan matsalar tsaro da habaka tattalin arziki da kuma noma.
“Batun yaki da cin hanci da rashawa wadanda suka ci amanarku za mu yi amfani da dokokin kasa, mu kwato abin da suka dauka ba bisa ka’ida ba a mai da shi baitul-mali a yi muku aiki da shi,” inji shi.
Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce idan har ’yan Najeriya suna goyon bayan yakin da ake yi da cin hanci da rashawa to kada su zabi PDP.
Ya ce APC tana yaki ne da barayi, “Babu wani mutumin kirki da zai so wadansu su samu damar ci gaba da cin hanci da rashawa. Don haka mu tabbatar ba mu bai wa masu neman wawushe dukiyar kasar nan damar cin zabe ba. Mu fito mu zabi APC kowa ya zabi APC,” inji shi.
Oshiomhole ya ce “Bisa abin da muka gani yau a Bauchi, tun yanzu mun yi nasarar lashe zaben 2019. Don haka ina sake nanata kira gare ku kowa ya tabbatar ya zabi dukan ’yan takarar APC a dukan matakai daga kasa har sama a yi sak!”
Mai masaukin baki, Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya nemi jama’a su fito su zabi ’yan takarar APC daga sama har kasa, domin su samu nasarar cimma muhimman ayyukan da suka faro a wa’adin farko.
Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jiharsa cewa kada su yarda da yaudarar da PDP take zuwa musu da su, ya ce ba su da wasu kyawawan manufofi na kyautata rayuwar jama’ar jihar.
Sai ya yaba wa jiga-jigai a siyasar Bauchi da suka dawo APC, ya ce za su hada karfi da karfe domin samun nasarar dawo da Shugaban Buhari da Gwamna M.A da sauran ’yan takarar APC a duk fadin kasar nan.