✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai sauya wa Katsina United motar da aka lalata musu

Gwamnan ya yi alkawarin saya wa Katsina United sabuwar mota.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi Allah wadai da yadda wasu bata-garin magoya kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka farfasa wa kungiyar Katsina United mota a satin da ya gabata.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Abba Anwar ya fitar a ranar Laraba, cewa gwamnan ya fusata da aka yi wa Katsina United mota.

“A matsayinmu na gwamnati mun yi Allah wadai da abin da ya faru kuma mun kafa kwamitin bincike.

“Muna fatan wannan al’amari ba zai shafi alakar Katsina da Kano ba saboda akwai dangantaka mai dimbin tarihi a tsakaninmu,” a cewar gwamnan.

Fusatattun magoya bayan Kano Pillar su tsaida wasan ne a minti na 79, suka shiga cikin filin wasan suka wa motar Katsina United kaca-kaca da kuma wani sashe na motar ’yan wasan Kano Pillars.

Wasan shi ne irinsa na farko da Masu Gida suka doka a Filin Wasa na Sani Abacha bayan tsawon shekara biyu suna buga wasa a waje.

Tuni dai aka ci tarar Kano Pillars kudi Naira miliyan tara tare da rage mata maki uku a Gasar Firimiyar Najeriya.