Gwamnatin Kano ta bayyana kudurinta na gina rukunin gidaje biyar a masarautun jihar na Kano, Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.
Kwamishinan Sufuri da Gidajen jihar, Mahmud Muhammad, ya sanar da haka yayin karin haske kan kasafin ma’aikatarsa ga Majalisar Dokokin jihar.
- HOTUNA: Gwamnatin Kano ta lalata barasar Naira miliyan 200
- An sace dan wan tsohon sarkin Kano Sanusi
- An cafke masu tallan maganin gargajiya 13 a Kano
- Yadda ’yan kwana-kwana suka ceto mutum 132 a Kano
“A kasafin 2021 mun ware biliyan N3.2 domin gina gidaje da kuma sayar da su cikin rahusa.
“Mun sake ware niliyan N3 domin samar da hasken lantarki na titin jirgin kasa, sai miliyan 200 domin tallafa wa masu harkar sufuri”, cewar Kwamishinan.
Muhammad ya ce an ware miliyan N30 daga cikin kasafin domin fara aikin gina gidajen a dukkannin masarautun.
Kwamishinan ya kara da cewa gina gidajen na daga cikin tsarin gwamnatin jihar na samar da gidaje cikin rahusa ga al’ummar jihar.
Ya kuma ce an kai kudurin Naira biliyan uku domin samar da hasken wutar lantarkin titin jirgin kasa.