✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje zai gabatar da kasafin kudi a majalisa ranar Talata

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya aike da takarda ga Majalisar Dokokin jihar yana bukatar ta ba shi dama ya gabatar da kasafin…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya aike da takarda ga Majalisar Dokokin jihar yana bukatar ta ba shi dama ya gabatar da kasafin kudin badi.

A ranar Litinin da safe Shugaban Majalisar Abdulaziz Gafasa ya karanta takardar gwamnan, sannan ya bayyana cewa ranar Talata gwamnan zai je ya gabatar da kasafin.

Tun da farko dai, an sanar da cewa Gwamna Ganduje zai gabatar da kudurin kasafin kudin ne ranar Litinin.

Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman Majalisar Zartawar Jihar na mako-mako a ranar Larabar makon jiya.

Kwamared Muhammad Garba ya ce tangarada aka samu wajen aikewa da takardar ga Majalisar Dokokin.