✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai dauke Gidan Zoo daga Kano

Gwamnatin Jihar Kano za ta sauya wa gidan ajiye namun daji (Gidan Zoo) na jihar matsuguni daga cikin garin Kano zuwa wani wuri na daban.…

Gwamnatin Jihar Kano za ta sauya wa gidan ajiye namun daji (Gidan Zoo) na jihar matsuguni daga cikin garin Kano zuwa wani wuri na daban.

Kwamishinan Raya Al’adu da Adana Kayan Tarihi na jihar, Ibrahim Ahmad ya ce za a komar da gandun namun dajin ne Karamar Hukumar Bebeji.

Ibrahim Ahmad, ya bayyana a ranar Laraba cewa za a mayar da gidan zoo din ne garin Tiga da ke karamar hukumar ta Bebeji.

Kwamishan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin dauke dabbobin da sauya matsugunin nasu daga cikin Jama’a ne zuwa wani wurin da ba za a dame su ba, saboda dabbobin basa son hayaniya da yawa.