✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagoyar ranar haihuwa

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon Gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Kwankwaso ya cika shekara 63…

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon Gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Kwankwaso ya cika shekara 63 da haihuwa a yau Talata 22 ga watan Oktobar bana.

Gwamna Ganduje, ya yi addu’ar Allah Ya karawa Kwankwaso lafiya da nisan kwana.

Kamar yadda Gwamnan ya sanar, “A matsayina na Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da gwamnatin jihar Kano tare da jama’ar Kano na taya tsohon Gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.