✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyin fadan daba a Kano

Ganduje ya ce zai hukunta duk wanda aka samu da daukar nauyin fadan daba.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin hukunta ’yan siyasa da ke daukar nauyin fadan daba a fadin jihar.

Ya bayyana cewar daukar matakin ya zama tilas, duba da yadda wasu bara gurbin ’yan siyasa ke son mayar da jihar dandalin fadan daba.

  1. An dakile yunkurin sace daliban sakandare a Kaduna
  2. An sace dalibai da malamai a Kwalejin Nuhu Bamalli ta Zariya

Ganduje ya yi wannan gargadi ne lokacin da wasu ’yan daba suka fito da makamai yayin da aka gudanar da wani taro a dakin taro na ‘Coronation Hall’ da ke Fadar Gwamnatin Jihar a wannan mako.

Aminiya ta rawaito cewar gargadin na zuwa ne awanni kadan bayan wani artabu da aka yi tsakanin magoya bayan Sanata mai wakiltar shiyyar Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo, yayin kaddamar da wani aiki a kan hanyar Gwarzo zuwa Dayi.

Gwamnan ya ce “Ba za mu lamunci wannan ba, kuma ina tabbatar muku da cewar za mu sa kafar wando daya da duk wanda suka karya wannan gargadi.”

Wakikinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya tursasa gwamnan yin wannan gargadi na da nasaba ne da yadda a lokacin magoya baya ’yan siyasar suka dinga zaro muggan makamai da sunan nuna kauna ga iyayen gidansu.

Gnduje ya kara da cewa “Ina sanar da ku cewar za mu yi bikin Ranar Dimokuradiyya a ranar Asabar, wanda Shugaban Riko na jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da wasu shugabanni za su kawo mana ziyara.

“Don haka na dakatar da dukkan wasu taruka na siyasa a fadin jihar nan.

“Duk wanda aka kama ya fito da wani makami a lokacin bikin gwamna zai hukunta shi da kansa.

Ya kara da cewar “Mun umarci dukkan Shugabannin Kananan Hukumomi da su tabbatar da ababen hawan da za a zo da su wajen taron ba sa dauke da makamai, sannan su gujewa lika hoton dan siyasa wanda hakan na iya tada tarzoma.

Gwamnan cikin fushi ya yi rantsuwa tare da alwashin daukar mataki “Wallahi Tallahi ba zamu lamunci wannan shirmen ba.”

Kazalika, ya sake shan alwashin hukunta ‘yan siyasar da ke daukar nauyin fadan daba a sunan neman takarar kujerar gwamnan jihar a babban zabe mai zuwa a 2023.