Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sauya wa Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST) da ke Wudil a Jihar, suna zuwa na hamshakin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote.
Daukar matakin, a cewar Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa Jihar ne yayin zamanta na mako-mako.
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa
- 2023: Dole APC ma ta kai takararta Arewa ko ta riga rana faduwa — Orji Kalu
Ya ce hakan kuma na cikin shawarar da Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta bayar.
Muhammad Garba ya tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Sanarwar ta ce yanzu za a rika kiran sunan makarantar da sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUST) da ke Wudil.
Kwamishinan ya ce tuni aka aike da bukatar canza sunan a hukumance ga Majalisar Dokokin Jihar ta Kano domin ta amince da shi ya zama doka.
Alhaji Aliko Dangote, wanda shi ne attajiri mafi kudi a nahiyar Afirka dai dan asalin Jihar ta Kano ne.
Jami’ar kuma a daya bangaren na daya daga cikin jami’o’i guda biyu mallakin gwamnatin Jihar.
Ko a shekarar 2018 sai da Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya canza wa Jami’ar Northwest, ita ma mallakin Jihar suna zuwa Yusuf Maitama Sule.