✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya nada sabuwar Shugabar Hukumar Kawata birnin Kano

Nadin nata ya biyo bayan neman kujerar takarar shugaban karamar hukumar Ungogo da Daraktan hukumar Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya shiga.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada Hadiza Ahmad Tukur a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kula da Birnin Kano.

Nadin nata ya biyo bayan neman kujerar takarar Shugaban Karamar Hukumar Ungogo da Daraktan-Janar din Hukumar, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya shiga.

Injiniya Hadiza, wacce ita ce Manajan-Daraktar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO), yanzu za ta kara da kujerar Darakta-Janar na Hukumar Kula da Birnin Kano.

Sanarwar ta fito ne daga Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, inda ya ce nadin nata zai fara aiki nan take.

Ya kara da cewa ana sa ran Hadiza za ta kawo sabbin tsare-tsare da za su kawo wa jihar Kano ci gaba fiye da na baya.