Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada Hadiza Ahmad Tukur a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kula da Birnin Kano.
Nadin nata ya biyo bayan neman kujerar takarar Shugaban Karamar Hukumar Ungogo da Daraktan-Janar din Hukumar, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya shiga.
- Masu siyar da jaridu a Kano sun taya Kabiru murnar zama Shugaban kungiyar NPAN
- Yadda aka daura auren matashin Kano da Ba’amurikiya
- Za a gina wa malaman makaranta gidaje 5,000 a Kano
- COVID-19 ta sake bulla a Kano, ta kashe mutum biyu
Injiniya Hadiza, wacce ita ce Manajan-Daraktar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO), yanzu za ta kara da kujerar Darakta-Janar na Hukumar Kula da Birnin Kano.
Sanarwar ta fito ne daga Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, inda ya ce nadin nata zai fara aiki nan take.
Ya kara da cewa ana sa ran Hadiza za ta kawo sabbin tsare-tsare da za su kawo wa jihar Kano ci gaba fiye da na baya.