Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon Sarkin Gaya.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da nadin a cikin wata sanarwar da safiyar ranar Lahadi.
- Afghanistan: Taliban ta rataye masu garkuwa a tsakiyar gari a matsayin jan kunne
- An kashe mutum biyu, an sace malamin tsangaya da wasu da dama a Zariya
Kafin nadinsa, sabon Sarkin, wanda da ne ga marigayi Sarki Ibrahim Abdulkadir da ya rasu ranar Laraba, shi ne ke rike da sarautar Ciroman Gaya.
Masarautar Gaya dai na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da Gwamna Ganduje ya daga likafarsu a shekarar 2018.
A cewar sanarwar, “Gwamna Ganduje, ya yi amfani da damar da dokar masarautu ta Jihar Kano ta 2020 wacce aka yi wa kwaskwarima ta ba shi wajen nadin Alhaji Ibrahim Aliyu Abdulkadir a matsayin sabon Sarkin Gaya.
“Hakan, ya biyo bayan shawarar masu nada sarki na masarautar bayan sun gabatar da sunan mutum uku, wanda daga ciki Gwamna ya amince da sunan Aliyu Ibrahim matsayin sabon sarkin,” inji sanarwar.
Daga nan sai Ganduje ya taya shi murnar tare da yi masa fatan alheri.