✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya nada sabbin manyan sakatarori 12

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabbin manyan sakatarorin ma’aikatu 12 da za su fara aiki nan take. Cikin wata sanarwa mai dauke da…

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabbin manyan sakatarorin ma’aikatu 12 da za su fara aiki nan take.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, gwamnan ya ce sai da duk sabbin sakatarorin suka bi matakai na tantancewa daban-daban, kafin ba su matsayin.

Sanarwar ta kuma ce za a rantsar da su ne ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar da karfe 2:00 na rana.

Wadanda aka bai wa matsayin sun hada da Injiniya Masur Yakubu, tsohon Darakta a ma’aikatar Ayyuka; Salisu Dan Azumi, Darakta a  Ma’aikatar Kananan Hukumomi; Saadatu Sa’idu Bala, tsohuwar Darakta a Ma’aikatar Lafiya.

Sauran sun hada da tsohon Sakataren Hukumar kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha, Ahmad Tijjani Abdullahi; Baba Sharu Dala, Darakta a Hukumar Karbar Korafe-Korafe; Aliyu Yakaubu, Darakatan ma’aiktar yawon bude idanu ta jiha.

Kazalika akwai Abbas Sunusi, Dokta Tijjani Hussain, tsohon Sakataren Hukumar Asibitocin Sha Ka Tafi; Nuhu Amasaye tsohon Darakta a Ma’aikatar Kananan Hukumomi; Aisha Kailani; Mustapha Madaki Huguma; sai Musa Tanko Garko daga ofishin Shugaban Ma’aikatan jihar.