Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon taken Jihar, domin karfafa kishin Jihar a tsakanin mutanen cikinta.
Bayanin hakan ya bulla ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Watsa Labaran Gwamnan, Abba Anwar, ya fitar ranar Lahadi inda ya ce gwamnatin na yin duk mai yiwuwa don ganin ta adana tarihi da al’adu, hadi da ci gaban jihar.
- Bayan ficewa daga tafiyar Tinubu, Naja’atu ta koma wajen Atiku
- NAJERIYA A YAU: Kwana 8 Kafin A Daina Karbar Tsoffin Kudade, Shin Sabbin Sun Zo Hannun Ku?
An rera taken ne dai da harshen Hausa.
Yayin bikin kaddamarwar da taken wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya yaba wa mai dakinsa, Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wacce ita ce ta assasa samuwar taken.
“Za mu kai taken gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano don a yi masa doka. Kuma idan hakan ta faru duk wani taro da za mu yi za a dinga rera taken bayan an kammala na kasa,” in ji Ganduje.
Ya kuma ce, “Taken dai na nuna yadda jihar ta yi shura a bangaren kasuwanci da sarauta da noma da karbar baki da sauransu.