✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘farfaganda’

Jarumi a masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da nadin a shafinsa na Instagram.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada fitaccen jarumin nan na masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Mustapha Naburaska a matsayin mai ba shi shawara kan ‘farfaganda’.

Jarumi, kuma mai shirya fina-finai a masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da nadin a shafinsa na Instagram ranar Lahadi, inda ya taya shi murnar samun matsayin.

Falalu ya ce an gudanar da bikin nadin ne yayin wata walimar cin abincin dare da ta gudana a Gidan Gwamnatin Kano da maraicen Asabar.

A baya dai, ana ganin Naburaska a matsayin wanda ba ya yin tafiyar Gwamna Ganduje, inda hatta wakoki da bidiyoyi ya sha daukar nauyi na dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, gabanin zaben 2019 da ya gabata a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sai dai ko kafin wannan nadin, jarumin ya ce a yanzu sun riga sun shirya da Gwamnan, yana mai cewa ko a baya ma wasu ne suka shiga tsakaninsu sannan suka hana ruwa gudu.

Kazalika, Gwamnan ya kuma nada Malam Khalid Musa a matsayin babban mai taimaka masa a bangaren harkokin masana’antar ta Kannywood.

A cewar Falalu Dorayi, “Muna godiya da wannan mukamai guda biyu. 1. Senior Special Assistant Kannywood (Malam Musa Khalid) 2. Special Adviser on Propaganda to the Governor (Mustapha Badamasi Naburaska).

“Jiya [Asabar] bayan kammala dinner da Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika mukamai guda biyu ga ’yan uwanmu.

“Daga yau duk wani mai bukata ko matsala tsakanin Kannywood da gwamnati to a nemi wadannan mutum biyu. Allah Ya taya ku riko, Ya baku ikon gamawa cikin amana da alkairi,” inji Falalu Dorayi.