✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada mahaifin Kwankwaso Mai Zaben Sarki

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya nada Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan jiahr, Rabiu Kwankwaso, a matsayin mai nadin sarki a Masarautar Karaye. Tsohon…

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya nada Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan jiahr, Rabiu Kwankwaso, a matsayin mai nadin sarki a Masarautar Karaye.

Tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso na daga cikin wadanda suka soki lamarin Ganduje na raba Masarautar Kano zuwa biyar.

Kwankwaso ya kasance uban gida ga Ganduje, kafin daga bisani adawa ta shiga tsakaninsu, har suka raba hanya a siyasa.

A ranar 5 ga Disambar 2019, Ganduje ya rattaba wa sabuwar dokar kafa sabbin masarautu biyar a Kano hannu, wanda ya ba shi damar kirkirar sabbin masarautun daga Masarautar Kano.

Sabbin masarautun su ne Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

Kakain Masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa, ya bayyana cewa Ahaji Musa Kwankwaso, mai rike da mukamin Makaman Karaye na daga cikin wanda za a yi wa nadin Masu Zabar Sarki a Masarautar Karaye a ranar Juma’a.

Sauran wanda za a yi wa nadin sarautar sun hada da; Sarkin Bai, Alhaji Jibrin Ibrahim-Zarewa; Sarkin Dawaki Mai-Tuta, Bello Hayatu-Gwarzo; Dan Iya, Bashir Mahe; da Madakin Karaye; Ibrahim Ahmad, kamar yadda ya bayyana a cikin jawabin da ya fitar.

Har wa yau, za a nada wadannan a matsayin mambobin majalisar: Walin Karaye, Isma’ila Gwarzo, tsohon Mai Bai Wa Marigayi Shugaban Kasa Janar Sani Abacha Shawara, kan tsaro; da Wazirin Karaye, Musa Muhammad; wadanda a yanzu suke manyan kansiloli a sabuwar masarautar da aka kirkira.

Ana sa ran Wazirin Sokoto, da wakili daga Masarautar Gwandu za su halarci bikin da aka shirya ranar Juma’a 27 ga Nuwamba, 2020 a Fadar Mai Martaba Sarkin Karaye.