Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya soke ayyukan gyaran titin Dawakin Tofa, da aka bayar tun shekaru takwas da suka wuce.
Bayan soke kwangilar daga kamfanin Rocad Construction Nigeria Limited , gwamnan ya bayar da aikin ga kamfanin CCECC na kasar China a kan Naira miliyan 651.9.
“Majalisar zartarwata kuma amince da sauye-sauye da kuma karin da aka samu a kudin aikin gyaran Gadar Bagauda a hanyar Wak-Tiga a Karamar Hukumar Bebeji”, inji Kwamishinan Watsa Labarai Muhammad Garba.
A shekarar 2012 jihar ta ba wa kamfanin Rocad aikin mayar da titin Dawakin Tofa mai hannu biyu, amma kamfanin ya yi watsi da shi tare da jefa ‘yan yankin cikin wahala.
Muhammad Garba, ya ce jihar ta kafa kwamitin duba yanayin tafiyar sauran ayyukan tituna masu hannu biyu a fadin jihar domin aunawa da sake tsari da kammalawa a kan kari ko kuma soke ayyukan titunan.