Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kori Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar, Dokta Muhammad Tahar Adam, wanda aka fi sani da Baba Impossible, daga mukaminsa.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar.
- Flossie: Kyanwar da ta fi tsufa a duniya ta cika shekara 27
- Tsohon Fafaroma Benedict XVI ya mutu yana da shekara 95
Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take.
A cewar sanarwar, Gwamna ya dakatar da Kwamishinan ne saboda wasu ayyukan rashin da’a, kuma ba ya yi wa bakinsa linzami.
Muhammad Garba ya ce dakataccen Kwamishinan na gudanar ayyukan ofishinsa kamar na kashin kansa.
Sanarwar ta kuma zarge shi da Baba Impossible ya cire Laraba da Juma’a daga ranakun aiki a ma’aikatarsa,
Ya ce tuni Gwamna Ganduje ya aike da sunan Dokta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero da ke Kano domin ga tantance shi a matsayin sabon Kwamishina.