✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya haramta tallata hotunan ’yan siyasa yayin bukukuwan Sallah a Kano

Ganduje ya ce babu bukatar tada zaune-tsaye yayin bukukuwan Sallah

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta wa magoya kowane dan takara tallata hotuna ’yan siyasa a yayin shagulgulan Sallah da za a yi.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labara na Jihar ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana kudurin Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje, ya ce daga yanzu an hana sanya tuta ko allunan ’yan siyasa yayin Sallar Idi da sauran taruka na bukukuwan Sallah don kaucewa barkewar rikici a tsakanin abokan hamayya.

Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin watan Ramadan da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin tarihi da al’adu, wanda ake zuwa kallo hatta daga kasashen ketare.

A cewarsa, don haka bai kamata a mayar da wadannan wurare wajen gangamin siyasa da yakin neman zabe ba, face yin abin da ya tara jama’a.

Ganduje ya jaddada cewa amfani da allunan siyasa a yayin taron da ya hada jama’a masu mabanbantan ra’ayi kamar Hawan Daushe, na iya haifar da tarzoma.

Sanarwar ta kuma umarci ’yan siyasa da su tabbatar sun yi biyayya sau da kafa ga sabuwar dokar zabe.

Gwamnan ya kuma taya daukacin al’ummar Musulmi murnar bikin sallah tare da fatan za su yi riko da abin da suka koya a watan Ramadan.

Har wa yau, Ganduje ya umarci jami’an tsaro da sanya kafar wando daya da duk wanda ya yi yunkurin karya dokar da Gwamnatin ta Kano ta shimfida yayin bukukuwan Sallah Karama da za a yi a fadin Jihar.