Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fitar da Naira biliyan 8.98 domin aikin ginin gadar sama a unguwar Hotoro da ke kan Babbar Hanyar Maiduguri.
Amincewar na zuwa ne bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar wa Shugaba Buhari taswirar gadar mai hawa uku, wadda kuma za a sa wa sunan Shugaban Kasar.
“A matsayin Kano na babban birni kuma cibiyar cinikayya a kasar nan, ana samun karuwar kai-komon ababen hawa; Hakan ya nuna akwai bukatar sauyawa da kuma inganta hanyoyinmu ta yadda za a samu tsaftatacce kuma amintaccen tsarin sufuri,” inji sanarwar ta ranar Talata.
- Buhari ya saki kudi kawai talaka ya ji dadi —Tinubu
- Kafin tafiyarsa London, Buhari na ganawa da Majalisar Tsaro
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, ya ce amincewa da fitar da N8,980,303,460.63 na aikin na daga cikin abubuwan da aka tabbatar a zaman Majalisar Zartarwar Jihar.
Yunkurin gina gadar ta jawo wa Gwamnatin Ganduje suka daga magabacinsa kuma tsohon maigidansa, Sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ya ce babu hikima a gina titin a halin yanzu.
“Kodayake da cewa akwai bukatar yin gadar sama a Kano, amma abin da mutane suka fi bukata a jihar shi ne ilimi.
“Ya kamata [gwamantin] su fi mayar da hankali wajen ganin ’ya’yanmu sun samu ingantaccen ilimi da ilimin sana’o’in dogaro da kansu,” inji shi.
Injiniya Kwankwaso, ya yi zargin akwai kura-kurai a taswirar gadar, wadda ya ce Shugaba Buhari bai ma fahimci zanen gadar wadda aikin Gwamnatin Tarayya ce gina ta.
“Maimakon Ganduje ya je ya nemi Shugaban Kasa ya yi gadar tunda aikin Gwamnatin Tarayya ne yin gadar ta da za ta hada birnin Kano da Wudil; sai ya kai masa hotunan da ba a tsara da kyau ba. Shugaban Kasa bai ma fahimta ba, alhali mun bar wanda ya fi wannan a ofishin,” inji Kwankwaso.